Ko me ya sa matasa ke kashe kansu a Ghana?

Gwamnatin kasar Ghana na nuna halin ko in kula da halin da al'ummar ta ke ciki na matsin tattalin arziki Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gwamnatin kasar Ghana na nuna halin ko in kula da halin da al'ummar ta ke ciki na matsin tattalin arziki

A kasar Ghana ana cigaba da samun karuwar mutanen da suke kashe kansu a 'yan makonnin nan.

Bayanai sun nuna a cikin makonni biyun da suka gabata an samu mutane goma da suka kashe kansu, cikinsu har da wasu dalibai mata.

Mafi yawancin wadanda suka kashe kan su a wannan lokaci dai mata ne.

Babban jami'i a hukumar kula da masu tabin hankali na kasar, Dr Akwasi Osei, ya ce wannan matsala ta wuce yadda ya ke tsammani, amma dai suna iya bakin kokarinsu domin shawo kanta.

A cikin shekarun baya-bayan nan dai an samu karuwar mutanen da ke kashe kansu musamman a tsakanin matasa maza da mata.

Masana a kasar na ganin cewar wannan matsalar ba ta rasa nasaba da tabin hankali ko kuma nuna halin ko in kula da gwamnatin kasar ke nuna wa talakawa.

Daga nan masanan, sun yi kira ga gwamnati da ta dauki matakan gaggawa wajen shawo kan wannan matsala.

Labarai masu alaka