'Illolin da auren dole kan haifar'

Auren dole ko na wuri na jefa mata da dama cikin mawuyacin yanayi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Auren dole ko na wuri na jefa mata da dama cikin mawuyacin yanayi

A Najeriya, auren dole na ci gaba da zama wata babbar matsala a tsakanin alumma, musamman a kasar Hausa inda za a aurawa yarinya miji ba tare da ta ganshi ko ta na sonsa ba.

Hakan dai ya kasance kamar al'ada a shekarun da suka shude.

An dai fi samun wannan matsala ta auren dole a yankunan karkara inda yarinya tun ta na karama za a zaba mata miji.

Wasu dai na kallon wannan al'ada ta auren dole a matsayin abin da bata dace ba, yayin da wasu iyayen kuma ke cewa suna da dalilansu na zabawa 'ya'yansu miji.

Iyayen sun ce wani lokacin sukan yi hakan ne domin karfafa zumunci a tsakaninsu, inda sukan hada aure a tsakanin dan wa da 'yar kani, ko kuma 'ya'yan aminai.

To sai dai kuma wasu kungiyoyi masu zaman kansu a Najeriya, na adawa da wannan al'ada kamar kungiyar Arida a jihar Kaduna.

Kungiyar ta ce wannan al'ada ce tun kaka da kakanni, kuma yanzu zamani ya canja, dan haka yakamata iyaye su rinka la'akari da yanayin zamani kafin su dauki mataki irin wannan.

Kungiyar ta cigaba da cewa, irin wannan aure na dole ko na wuri ba bu abinda ba ya haifarwa, wani lokaci matan kan kashe mazajen da aka aura musun, ko kuma su zuba musu guba a abinci, duk dai dan nuna kiyayyya ga aure.

Kazalika kungiyar ta ce irin wannan aure ya kansa yarinyar ko yaron wato ango wani daga cikinsu ya gudu ya shiga duniya.

Dan haka kungiyar ta yi kira ga iyaye da su yi hattara wajen auren dole ko na wuri bisa la'akari da matsalolin da ya ke haifarwa.

Labarai masu alaka