Kotu ta sake watsi da dokar hana musulmi shiga Amurka

Zababben Shugaban Amurka Donald Trump

'Yan sa'o'i kadan sabuwar dokar da shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba wa hannu, ta hana 'yan kasashen musulmai guda shida shiga Amurkar, ta fara aiki, wani alkali ya yi watsi da dokar.

Darren Watson dai ya yanke hukuncin ne bisa dogaro da cewa dokar ba wani abu za ta jazawa Amurkar ba, illa kyamata ga musulmai.

Wata kungiyar lauyoyin jihohin Amurka ce dai ta shigar da wannan kara kuma ta samu nasara.

Lauyoyin dai sun ce hana musulmai shiga Amurka ka iya haifar da wariya sannan kuma fannin yawon bude ido na kasar zai iya samun koma-baya da kuma samun karancin ma'aikata a kasar.

To sai dai kuma shugaba Trump ya bayyana al'amarin da wani abun da ba a taba yin irinsa ba a shari'ance.

"Kundun tsarin kasar ya ba wa shugaban kasa damar dakatar da masu cirani a duk lokacin da yake da bukatar yin hakan da manufar kare kasa." In ji Trump.

Mista Trump ya kuma lashi takobin kalubalantar shari'ar a kotun kolin kasar.

"Wannan hukuncin ya nuna cewa Amurka na da rauni, ni kuma na yi imanin ba haka ba ne. Ku dibi iyakokinmu ku gani. Za mu tunkari wannan danyen hukuncin.

Za mu je duk inda ake zuwa ko da kuwa kotun koli ne domin mu daukaka kara. Za mu yi nasara. Za mu kare 'yan kasarmu."

Dokar dai ta so hana musulmai daga kasashe shida shiga Amurka har na kwanaki 90 sannan kuma ta dakatar da 'yan gudun hijra shiga kasar na kwanaki 120.

Kasashen dai su ne Iran da Libya da Syria da Somalia da Sudan da kuma Yemen.

Hakkin mallakar hoto APTN
Image caption Donald Trump, ya ce, yana son tattaunawa da 'yan kasar ba tare da 'rairaye' abin da zai fada musu ba.

A baya dai Irin wannan dokar ba ta yi nasara ba bayan da wani alkalin wata kotu a birnin Seattle ya dakatar da ita.