An soki gwamnatin Ghana kan nada ministoci 110

Shugaba Akufo-Addo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Nana Akufo-Addo ya kara yawan ministocin gwamnatinsa

A kasar Ghana 'yan adawa sun soki yawan ministocin da gwamnati ta nada da ba a taba samun masu yawansu ba a tarihin kasar, ko da yake gwamnatin ta kare matsayinta.

Hakan na zuwa ne bayan shugaba Nana Akufo-Addo ya nada karin wasu ministoci 50 a ranar Laraba.

Karin da ya sa a yanzu kasar ke da ministoci 110.

Idan aka amince da sabbin ministocin da shugaba Nana Akufo-Addo ya gabatar , ministocin yada labarai da na makamashi da na aikin noma da kuma na kananar hukumoni dukkansu zasu samu mataimaka uku-uku.

A wata hira da kafofin watsa labarai, dan adawa Haruna Iddrisu ya soki yawan jami'ai gwamnati, inda yace zai janyo kashe kudin masu yawa.

Sai dai Ministan yada labarai, Mustapha Hamid ya mayar da martani da cewa "Gwamnati bata dauki alkawarin cewa ba zata dauki jami'ai da yawa ba."

Mista Hamid ta kara da cewa wajibi ne gwamnati ta samu jami'ai da yawa domin su taimaka wa shugaban kasa wajen aiwatar da manufofinsa.

An zabi Nana Akufo-Addo na jam'iyyar NPP, bayan ya yi takara har sau uku bai samu nasara ba.

Labarai masu alaka