Kenya na bukatan dala milliyan 116 saboda masalar fari — UN

Arewacin Kenya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Farin da ake fuskanta a arewacin Kenya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana bukatar dala miliyan 166 domin hana tabarbarewar matsaloli sakamakon farin da aka samu a arewacin Kenya.

Majalisar ta kara da cewa an shafe shekara uku ba a ruwan sama a yankin abinda ya janyo kishin ruwa da yunwa wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar dabbobi da yaduwar cututtuka a kasar.

Duk da matakin da gwamnati ta dauka a baya-bayan nan na aikawa yankunan da ke fama da yunwa kudade maimakon abinci, rashin abinci ya karu inda yawan 'yan Kenyan da ke fama da rashin abinci ya kai miliyan 2.6 cikin kasa da shekara daya.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa yara da mata masu juna biyu da uwaye fiye da 357,000 ba sa samun abinci masu gina jiki.

Ta kara da cewa al'amura ka iya ta'azara idan ba a samu ruwan sama ba nan gaba.

A watan da ya gabata ne Kenya ta shiga farin da ya shafi rabin kasar.

Labarai masu alaka