Wasu 'yan Ghana na shirin korar baki

Gwamnatin kasar Ghana ta sha alwashin kawo karshen matsalar kyamar baki Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamnatin kasar Ghana ta sha alwashin kawo karshen matsalar kyamar baki

Wani rikicin kyamar baki ya sake barkewa a yankin Banda dake jihar Brong Ahafo a kasar Ghana.

Rahotanni sun ce wasu da ke kiran kansu masu kishin yankin Banda, su ne suka lika wata sanarwa a jikin gine-gine, inda suke korafi cewa baki na kwace musu ayyukan yi.

Wannan ne ya sanya su neman bakin su bar yankin ko kuma su dandana kudarsu.

Sanarwar ta kara da cewa, abin da ya faru a kasar Afirka ta Kudu a 'yan makonnin da suka wuce, shi zai kasance ga duk bakin da suka yi saura a yankin.

A yanzu haka dai duk an rufe ma'aikatu da asibitoci da sauran ofisoshin gwamnati a yankin, a yayin da ma'aikatan da ba a 'yan asalin yankin ba ke ci gaba da tserewa.

Tuni dai aka tura karin 'yan sandan kwantar da tarzoma zuwa yankin.

A nasa bangaren, dan majalisar dokokin yankin, Malam Ahmed Ibrahim, ya ce da shi da sauran sarakunan yankin sun fusata da lamarin.

Domin haka ne kuma suka yanke shawarar ganawa da sarakunan da matasa da ma'aikata da kuma masu fada aji wajen lalubo hanyar kawo karshen wannan matsala.

A baya dai an taba samun irin wannan matsala, inda wasu ma'aikata da ba 'yan asalin yankin ba suka rasa rayukansu.

Sharhi, Aisha Shariff Baffa

Ghana dai ba ita ce kasa ta farko da aka fara nuna kyamar baki ba.

Afirka ta Kudu ma dai ta yi kaurin suna wajen wannan dabi'a, inda wasu 'yan kasar ke adawa da zaman baki 'yan ci rani saboda a ganinsu suna toshe musu damar samun ayyukan yi a kamfanonin kasar.

'Yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudun na daga cikin wadanda kyamar bakin ta shafa, lamarin da ya sa ake balla musu wuraren sana'a

'Yan Najeriya dai na yawon cirani a nahiyar Afirka da ma sauran sassan duniya.

Hakan kuwa ba ya rasa nasaba da irin yawan da suke da shi sakamakon kasar ce ta fi kowacce yawan jama'a a nahiyar Afirka.

Irin waccan kyamar ta baki dai a Afirka ta Kudu ta harzuka wasu 'yan Najeriyar da ke gida, inda suka rinka gudanar da bore a kan kin amincewa da abin da ake yi wa 'yan uwansu da ke zaune a Afirka ta Kudun.

Labarai masu alaka