Somalia: An sako jirgin dakon man da aka yi garkuwa da shi

A ranar litinin din da ta gabata ne akayi garkuwa da jirgin Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar litinin din da ta gabata ne akayi garkuwa da jirgin

Mahukunta a Somaliya sun ce an saki jirgin dakon man nan da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa dashi a kusa da gabar tekun kasar a ranar Litinin din da ta gabata.

An dai saki jirgin ne ba tare da biyan kudin fansa ba kamar yadda 'yan bindigar suka bukata a baya.

A cikin jirgin dai akwai 'yan kasar Sri Lanka takwas kuma an sake su ba tare da cutar da su ba.

Jirgin ruwan, samfurin MT Aris 13 na kan hanyarsa ne ta zuwa Mogadishu daga Djibouti a ranar 13 ga watan Maris, inda maimakon ya nisanta kanshi daga tekun Somaliyan, sai ya bi gajeriyar hanya dake tsakanin kuryar kusuwar Afirka da tsibirin Socotra da ke Yemen.

Masu fashin tekun Somaliyan sun far wa jirgin da wasu jiragen ruwa masu gudu sosai guda biyu, kilomita 17 bayan ya bar gabar tekun, yayinda suka rika nuna makamansu ga ma'aikatan jirgin ruwan.

'Yan fashin sun bar jirgin ne a wajen 'yan sanda masu tsaron ruwa bayan an cimma yarjejeniya.

Wannan ne karo na farko da 'yan fashin teku suka yi nasarar fashin jirgin ruwa, mai dakon mai na wata kasar tun a shekarar 2012.

A shekarar 2010 ne fashin teku ya yi kamari a Somaliya, a bangarorin sace-sacen jiragen ruwa da kuma ma'aikatansu da ake garkuwa da su domin karbar kudin fansa.

Labarai masu alaka