Shin harkar kera mutum-mutumi na cikin bukatun tsofaffi?

Mai maraba da baki a sashin ci gaban kafafan watsa labarai na IMI da ke jami'ar fasaha ta Singapore wata mutum-mutumiya ce mai dariya da aka sanya wa suna Nadine.

Hakkin mallakar hoto NTU Singapore
Image caption Nadine ta fara rayuwarta a matsayin mutm-mutumiya mai marabarat baki amma farfesa Nadia Thalmann ta yi imanin cewar za ta iya za ma mai kula da mutum.

Daga nesa babu wani abin mamaki a sifarta. Sai dai in ka matso kusa da ita za ka fara shakku. E mutun-mutumiya ce.

Nadine mutun-mutumiya ce mai basira sosai, wacce take da cikakken 'yancin dabi'a. Duk da cewa na'ura ce, siffarta da kuma halinta sun yi kama da asalin mutum.

Ta kan gane mutune tare da halin da suke ciki,kuma takan yi mu'amala da su, ta hanyar amfani da ilimin da aka shirya mata, wato abinda za a iya cewa tunaninta.

Har yanzu ana kara inganta kwarewar mai tarbar bakin ne a sashin cigaban kafafan watsa labarai na IMI. Amma na ba da jimawa ba Nadine za ta iya zama ma'aikaciyar jinya.

Raguwar yawan jama'a

Bincike game da amfani da mutum-mutumi domin aikin jinya ya fara yi nisa. Ba abin wahala ba ne a ga me ya sa haka.

Mafiya yawan mutanen duniya sun tsufa, hakan ya sa mutane sun yi wa shirye-shiryen kiwon lafiya yawa.

Duk da cewa tsofaffin mutanen da suka kai shekara 80 a duniya na bukatar abokan hira, ko wani wanda zai sanya ido a kansu ko da za su fadi. Yawancin tsoffaffi na fuskantar cututtuka masu tsanani kamar gigin-tsufa.

Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Abokan taka kaman na tsakanin Frank Langella da kuma mutum-mutumin da ke kula da shi a fim din 'Robot and Frank' ka iya zama abu mai yiwuwa a gaba.

Ta yaya za mu samar da ingantaccen kula domin biyan wadannan bukatun? Mafiya yawan masana na ganin cewa amsar nan ita ce mutun-mutumi.

Wata tawagar Farfesa Nadia Thalmann ke jagoranta ce take gina Nadine. Kuma sun shafe shekaru suna bincike amfani da fasahar Intanet wajen inganta mutane.Nadine kuma 'yar shekara uku ce.

Farfesa Thalmann ta ce game Nadine: "Tana iya aiki irin na mutane kaman gane mutane da farin ciki ko bakin ciki da kuma iya tuna mutane."

Nadine za ta iya sauya idan mutum ko yanayin da take hulda shi ya sauya abiunda ya sa ta dace da kula da tofaffin mutane.

Mutun-mutumiyar za ta iya kula da maras lafiya da kuma neman dauki a lokacinn gaggawa. Za ta iya hira da kaanta labarai da kuma buga wasannin kmfuta." Wannan mutun-mutumiyar ba ta gajiya ko kuma kosawa," in ji farfesa Thalmann. "za ta yi abin da aka ajiye ta ta yi."

Duk da haka, Nadine ajizi ce.Tana da matsalar fahimtar tasirin harshen mutun kan maganarsa, sannan kuma ba ta iya sarrafa hannayenta dai-dai .Amma dai Farfesa Thalmann ta ce mutun-mutumi za su iya fara kula da tsoffi nan da shekara 10.

Ba a shirya wa mutun-mutumi ba

Katafaren kamfanin fasahar kasar Amurka, wato IBM, tare da hadin gwiwar Jami'ar Rice dake birnin Houston a jihar Texas, su ma sun dukufa wajen samar da mutun-mutumi masu aikin jinya.

Sun samar da wani mutun-mutumi mai aiki da yawa wanda zai taimaka wa tsofaffi wato Multi-Purpose Eldercare Robot Assistant.

Hakkin mallakar hoto IBM Research
Image caption Dakin binciken IBM kan tsufa

Mera zai iya kula da zuciya da numfashin marar lafiya ta hanyar yin nazari kan bidiyon fuskarsa Zai iya gani idan mara lafiyan ya fadi kuma ya sanar da maus kula da lafiyarsa.

Amma ba kowa bane ya shirya wa mautum-mutumi mai kula da mutum ba, kamar yadda shugaban binciken IBM na dabarar bullo wa tsufa, Susann Keohane ya fada.

Wannan ra'ayi ya samu goyon bayan wani binciken Gartner wanda ya kin amfani da mutum-mutumi wajen kula da tsofaffi.

Sai dai mutane da dama ba su yarda mutun-mutumi su kula da iyayensu ba, duk da cewa yana rage kashe kudi , kamar yadda Kanae Maita shugabar masu binciken cigaba na binciken Gatner ya bayyana.