Cajin wayar salula ya kashe wani a banɗaki

Richard Bull Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Ƙwararru sun ce caza wayar salula a banɗaki yana tattare da hatsari musammam a lokacin da mutum yake tuɓe babu tufafi kuma ya yi wa jikinsa sharkaf da ruwa

Wani mutum ya rasu sakamakon jan lantarki a lokacin da yake cajin wayarsa a banɗaki, kamar yadda aka bayyana a sauraron wani bincike.

Richard Bull ya mutu yayin da cajar wayar iPhone ɗinsa ta taɓa ruwa a gidansa da ke Ealing, a yammacin London.

Mai binciken sanadin mutuwa ya yanke hukuncin cewa rasuwar Richard Bull hatsari, ce don haka ya shirya aika wani rahoto ga kamfanin ƙera wayoyin Apple don ya ɗauki matakin kare aukuwar haka a gaba.

Masu gangamin kiyaye lafiya sun yi gargaɗi a kan hatsarin caja wayoyin salula a kusa da ruwa sakamakon wannan bincike.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Richard Bull yana cajin waya a lokacin da lantarki ya ja shi

Jaridar the Sun ta ruwaito cewa an yi imani Mista Bull ya jona wayarsa ne a wata 'yar yawo daga falo kuma ya ɗora ta a kan ƙirjinsa lokacin da yake amfani da wayar.

Jaridar ta ce ya ji mummunar ƙuna a ƙirjinsa da hannu lokacin da cazar ta taɓa ruwa kuma ya mutu a ranar 11 ga watan Disamba.

Ƙungiyar 'Charity Electrical Safety First' ta ce mutuwar ta nuna wasu haɗurra da kayan lantarki ke da su a kusa da ruwa.

Manajan tabbatar da lafiyar kayan lantarki na Apple Steve Curtler ya ce "lantarki ba zai ja mutum ba" sakamakon amfani da na'urorin tafi da gidanka kamar laptop ko wayar salula matuƙar ba caza su ake yi ba.

Akasarin irin waɗannan na'urori suna da ƙarancin lantarki adadin boltej 5V zuwa 20V don haka "mai yiwuwa ba ma za ka ji ba" idan sun taɓa ruwa, a cewarsa.

Sai dai, jona wayar salula da caza ga wata babbar kafar lantarki na ƙara kasadar cutarwar da za su iya yi.

Labarai masu alaka