'Gagarumin ci gaba' kan cutar da ta addabi duniya

Likitoci na kokarin ceto wata maras lafiya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Miliyoyin mutane ne suke mutuwa a fadin duniya sakamakon bugun zuciya da shanyewar barin jiki

Wata sabuwar fasahar magani ka iya kare aukuwar bugun zuciya da shanyewar ɓarin jiki ta hanyar kankare kitse mai yawan gaske, a cewar likitoci.

Sakamakon gwajin da aka yi wa maras lafiya dubu 27 a faɗin duniya, na nufin nan gaba kaɗan za a iya amfani da shi a kan miliyoyin mutane.

Wata cibiya mai suna British Heart Foundation ta ce binciken wani muhimmin abu ne wajen yaƙi da babbar cutar da ke hallaka ɗan'adam a duniya.

Kimanin mutum miliyan 15 ne ke mutuwa duk shekara sakamakon bugun zuciya da shanyewar ɓarin jiki.

Maiƙon cholesterol mugun abu ne ga zuciya - don yakan cushe hanyoyin jini, ta yadda cikin sauƙi jini zai iya katsewa, ya jefa zuciya cikin mawuyacin hali, ƙwaƙwalwa kuma ta kasa samun numfashi mai ni'ima.

Wannan ce ta sa miliyoyin mutane ke shan wani magani da ake kira statins don rage yawan baƙin maiƙon cholesterol.

Wannan sabon magani - evolocumab - na sauya yadda hanta take aiki ta yadda kuma za ta iya kankare baƙin maiƙon cholesterol.

Farfesa Peter Sever na Imperial College London ya ce "Maganin ya fi statins tasiri matuƙa da gaske."

Farfesa Sever wanda ya shirya gwajin da aka yi Burtaniya da tallafin wani kamfanin haɗa magunguna Amgen ya faɗa wa BBC cewa: "Sakamakon ƙarshe da aka samu shi ne yawan maiƙo ya ragu sosai da sosai, ya yi raguwar da ba mu taɓa ganin irinta ba kafin gwada wannan magani."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Farfesa Peter Sever na Imperial College London ya ce "Maganin ya fi statins tasiri matuƙa da gaske."

Marasa lafiyan da aka yi wa gwajin da ma suna amfani da statins amma sai sabon maganin ya taimaka musu wajen sake rage kasadar da suke fuskanta.

Farfesa Sever ya ƙara da cewa: "Sun sake samun raguwar kashi 20 cikin 100 ta kasadar da suke ciki kuma wannan babban al'amari ne. Mai yiwuwa ma shi ne sakamakon gwajin maganin rage maiƙon cholesterol mafi muhimmanci da aka taɓa yi a sama da shekara 20."

An wallafa binciken a mujallar New England Journal of Medicine kuma an ba da rahoton sakamakon a taron ƙwararrun likitocin zuciya na kwalejin Amurka.

Nazarin ya nuna cewa an iya kare aukuwar bugun zuciya ko shanyewar ɓarin jiki ɗaya a cikin duk maras lafiya 74 da suka sha maganin a wannan gwaji na tsawon shekara biyu.

Sai dai ya yi wuri a iya sanin ko maganin zai ceto rayuwa.

Yaya yake aiki?

Maganin Evolocumab garkuwar jiki ne tamkar makaman da jiki yake da su don yaƙi da cutuka.

Sai dai, an tsara shi ne yadda zai far wa wani sinadarin abinci mai gina jiki wato protein da ake samu a hanta wanda ake kira PCSK9.

Daga bisani za ta ƙarfafa hanta ta hanyar ragargaza baƙin maiƙo a cikin jini.

Sauran wasu gwaje-gwajen sun nuna yadda garkuwar jikin ta kankare maiƙo da kashi 60 cikin 100.

Ana ba da maganin ne ta hanyar allura wadda ake yi a duk mako biyu ko huɗu.

Sai dai, Farfesa Sever ya ce: "Mai yiwuwa sabon maganin ba zai maye gurbin statins ba, akwai ɗumbin mutane masu yawan maiƙo a duniya, don haka ga alama ana buƙatar magani fiye da ɗaya don rage yawansa a jiki."

Kuɗin maganin dai ya sha bamban, amma ana kyautata zaton masu inshorar lafiya a Burtaniya ka iya samunsa a kan fam dubu biyu a shekara ga maras lafiya, kuma tuni aka fara ba wa marasa lafiyan da statins, ya gaza yi musu wani tasiri.

Labarai masu alaka