Za a koyawa dalibai tantance labaran bogi a kafafen sada zumunta

Dalibai Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dalibai na amfani da kafofin sada zumunta don gano muhimman bayanai

Wata babbar cibiyar bincike a duniya, ta ce akwai bukatar makarantu su koyawa dalibai dabarun gano labaran bogi da yadda za su iya gane karyar da aka yi a kafafen sada zumunta na zamani.

Kungiyar hadin kai da bunkasa tattalin arziki OECD, za ta gabatar da tambayoyi da kuma yin duba sosai a kan kafofin sada zumunta na zamani, ta kuma gano bayanan karya a wani gwaji da za ta yi nan gaba, wanda zai samar taimakawa matakan ilimi a fiye da kasashe 60.

Shugaban bangaren ilimi na kungiyar OECD, Andreas Schleicher, ya ce dalibai sun dogara sosai kan samun bayanai daga intanet da kafofin sada zumunta, wanda hakan ya sa ake samun matsala wajen samo ainihin sahihan bayanan da ake bukata, irin na manyan littatafai.

Tun bayan samuwar kafofin sada zumunta na zamani dai ana yawan samun matsala ta yada bayanan karya da kuma labaran kanzon-kurege sosai a kafofin.

Babbar matsalar kuma ita ce ta yadda mutane suka fi son samun bayanai daga kafofin sada zumuntar fiye da na kafafen yada labarai na ainihi.

Labarai masu alaka