Ba mu damu da barazanar Trump ba — OPEC

OPEC Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption OPEC ta ce tana da yakinin kasuwar mai za ta kara inganta a duniya

A baya-bayan nan, wasu manyan kasashe da ke kan gaba ta fuskar sayen man fetur irin su Amurka da China sun bayyana aniyar sauya hanyoyin da suke samun makamashi ga masana'antunsu.

Ga misali Amurka ta ce za ta dogara kan man da za ta rika haka a cikin gida da kuma wanda tuni ta saya ta jibge.

Matakin na zuwa ne yayin da a bangare guda, kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC, da hadin gwiwar wasu manyan kasashe da ke da man amma ba su cikin kungiyar irin su Rasha, ke kokarin aiwatar da wata yarejejniya da suka cimma a karshen shekarar da ta gabata.

Yarjejeniyar na da nufin rage adadin man fetur da suke kai wa kasuwa, ta yadda farashinsa zai tashi don amfanin duk kasashe masu arzikin man.

Wasu kasashe na kungiyar ta OPEC dai kamar Nijeriya da Iran da Libya an yafe masu wajibcin rage adadin man saboda da irin manyan kalubale da suke fuskanta, ko dai ta fuskar tsaro ko kuma ta fuskar tattalin arziki, domin idan aka ce su ma su rage adadin mai da suke sayarwa, hakan zai kara jefa su cikin mawuyacin hali.

Kungiyar ta OPEC ta kuma ce tana fata kasashen Afirka da suka samu man fetur a baya-bayan nan, irin su Nijar da Ghana za su shiga cikin kungiyar.

Yayin wata ziyarar aiki a London kwanan baya, Babban Sakataren kungiyar ta OPEC, Alhaji Muhammad Sanusi Barkindo, ya fara da yi wa Is'haq Khalid bayani kan inda aka kwana game da rage adadin man fetur a kasuwar duniya.

Ga yadda hirar tasu ta kasance:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Gane Mani Hanya

Labarai masu alaka