Chelsea ta doke Stoke City 2-1

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Chelsea ta yi zarra

A ci gaba da wasannin Firimiyar Ingila, a yau Chelsea ta doke Stoke City da ci 2 - 1a wasan da aka buga a filin wasa na Bet365 Stadium.

Dan wasan Chelsea Willian ne ya fara jefa kwallo a minti na 13, yayin da Gary Cahill ya kara ta biyu a minti na 87.

A nata bangare kuma, dan wasan Stoke City Jonathan Walters ne ci mata kwallo a bugun da fenareti a minti na 38.

Wannan sakamakon ya sa Chelsea sun cira gaba da maki 13 yayin da ya kasance saura wasanni goma.