Ashe saƙon Twitter zai iya ta da farfaɗiya?

A Twitter Post Hakkin mallakar hoto ARI GOLDSTEIN
Image caption Hoton wanda aka aika ta shafin Twitter yana dallara haske

An kama wani mutum bisa zargin aika wani hoto ga wani marubuci don tayar masa da farfaɗiya, a cewar ma'aikatar shari'ar Amurka.

A cikin watan Disamban bara ne, John Rayne Rivello, mai shekara 29, a jihar Maryland ya aika wa Kurt Eichenwald wani hoto ta shafin Tweeter wanda a jiki akwai wani haske da ya dallare, da ka iya sanya farfaɗiya.

Jaridar New York Times ta ce an caji John Rivello da laifin bin diddigin wani a intanet kuma yana iya fuskantar ɗaurin shekara goma a gidan yari.

An zarge shi da rubuta "Allah ya haɗa ka da farfaɗiya saboda abin da ka wallafa."

An dai san Mista Eichenwald da larurar farfaɗiya.

Babban marubuci ne a wata mujalla mai suna Newsweek, kuma edita a jaridar Vanity Fair kuma shahararren mawallafin litattafai ne.

Masu bincike sun gano cewa Mista John Rivello ya aika wa wasu masu Twitter saƙwanni game da marubucin, har yana faɗa musu shirinsa na far masa, a cikin saƙwannin akwai wani da ke cewa: "Ina fatan wannan zai sanya shi farfaɗiya".

'Sakon tamkar wani bam ne da akan aika cikin ambulan'

A cewar ma'aikatar shari'ar Amurka akwai ma wani saƙo da ke cewa "Mu tura masa wannan mu gani ko zai mutu."

Haka zalika, masu bincike sun gano wani hoto da ya ɗauka a wani shafinsa na sada zumunta inda ya jirkita tarihin Mista Eichenwald a Wikipedia, ta hanyar rubuta 16 ga watan Disamba a matsayin ranar mutuwarsa.

John Rivello ya kuma yi bincike kan abubuwan da ke tayar da farfaɗiya a shafin intanet na epilepsy.com website.

Lauyan marubucin, Steven Lieberman ya ce saƙon ba shi da maraba da "saƙon bam da ake aikawa ta gidan waya ko kuma hodar anthrax da ake aikawa nannaɗe a cikin ambulan. Yana da wani tasiri a jiki."

Ma'aikatar shari'ar ba ta ce ga abin da ya janyo wannan farmaki na intanet ba, ko da yake rahotanni na bayyana raɗe-raɗin cewa hakan mai yiwuwa na da alaƙa da yadda Mista Eichenwald ke sukar shugaban Amurka, Donald Trump a Twitter.

Bayan wannan al'amari, Stefano Seri, wani farfesa kan nazarin lafiyar tsikokin jiki a jami'ar Aston ta Burtaniya, ya ce an tsara abubuwan da hoton ya ƙunsa ne cikin tsanaki.

A cewarsa "Sauyin tafiyar haske bagatatan ka iya tayar da farfaɗiya..."