Bai kamata duniya ta manta da mu ba - 'Yar Chibok

Chibok Schoolgirls
Image caption Kimanin shekara uku kenan da sace 'yan matan Chibok kuma har yanzu ba a kubutar da mafi yawansu ba

Wata 'yar sakandaren Chibok da ta kuɓuta daga hannun 'yan tada-ƙayar-baya a Nijeriya ta yi kira ga al'ummar duniya cewa kada a manta da takwarorinta da har yanzu ke hannu.

A cikin watan gobe ne za a yi juyayin cika shekara uku da sace 'yan matan su fiye da 270.

Har yanzu mayaƙan Boko Haram na riƙe da 'yan matan da suka sace 195.

Ɗalibar wadda ta yi jawabi ga wani taron ilmi da aka shirya a Dubai ta ce: "Waɗannan 'yan mata, 'yan'adam ne, ba abu ne da za a manta kawai da shi ba."

Sace 'yan matan sakandaren Chibok a ranar 14 ga watan Afrilun 2014 a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya ta janyo kiraye-kirayen al'ummar duniya da kuma harzuƙa gangami kan ilmin mata.

Ɗaya daga cikin 'yan matan, wadda ke amfani da sunan "Sa'a" don kada a shaida ta, ta ce "sai duniya ta yi wani abu" don ceto ƙawayen karatunta.

Ta ce "Yaya za ka ji idan aka ce 'yarka ko matarka ta ɓata? Ba ɓatan kwana ɗaya ko biyu ba, shekara uku. Abin akwai takaici."

Labarai masu alaka