Nigeria: An kama mutum 34,000 da laifin ta'ammali da kwaya

NDLEA Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption NDLEA ta kama mutum 34,499 da laifukan da suka shafi tu'ammali da miyagun kwayoyi cikin shekara hudu

Hukamar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta kama mutum 34,499 kan laifukan da suka danganci tu'ammali da miyagun kwayoyi a jihohi 36 da kuma babban birnin kasar daga tsakanin shekarar 2012 zuwa 2015.

A wani rahoto da ta fitar, NDLEA ta ce jihar Kano da ke Arewa maso Yamamcin kasar ce kan gaba wajen yawan masu amfani da kwayoyin da ke sa maye, sai jihar Katsina ta biyu, sai jihar Filato ta uku da kuma jihar Ekiti ta hudu.

Kwamandan hukumar ta reshen jihar Kano, Hamza Umar, ya shaida wa BBC cewa mafi yawan mutanen da aka kama da laifin, masu shan kananan kayan maye ne irin su Tramol da magungunan tari da ake sha ba bisa ka'ida ba.

Ya kuma ce jihar Kano ta zama kan gaba ne saboda ita ce ta fi ko wacce jiha yawan al'umma.

Haka kuma shiyyar Arewa maso Yamman ce aka fi samun laifukan fiye da sauran shiyyoyin kasar biyar, inda aka samu masu laifin ta'ammali da kwayoyin har 8,939.

Shiyyar Kudu maso Yamma ce ta biyu da laifuka 6,999, sai shiyyar Arewa ta Tsakiya da laifuka 5,574,

Ta hudu ita ce shiyyar Kudu maso Kudancin kasar inda aka samu laifuka 5,545.

Shiyyar Kudu maso Gabashin kasar ce ta biyar da laifuka 4,230 sai kuma shiyyar Arewa maso Gabas da laifuka 3,212.

Wata mujallar bincike mai suna Economic Confidential, ta ce, "kasancewar shiyyar Arewa maso Gabas wadda take da karancin aikata irin wannan laifi zai bayar da mamaki, ganin cewa an shafe shekaru ana fama da hare-haren masu tayar da kayar baya."

Wani sharhi da aka yi na sosai a kan rahoton ya nuna cewa daga cikin masu laifin ta'ammali da miyagun kwayoyi 32,499 din aka kama, fiye da 32,000 duk maza ne, inda kasa da 2,000 kuma suka zamo mata.

Hakan na nuna cewa maza ne suka fi aikata laifukan da suka shafi tu'ammali da miyagun kwayoyin cikib shekara hudun da aka shafe ana wannan bincike.

Mista Umar ya kara da cewa, a cikin shekara hudun da ta gabata, yawan miyagun kwayoyin da hukumar NDLEA ta kwace daga jihohi daban-daban ya kai ton 40.

"Amma daga cikin ton 40 dinnan, kilo daya ne kawai na mugayen kwayoyi irin su koken, sauran duk kananan kwayoyi ne," in ji shi.

Ya ce, "A yanzu haka tuni hukumar ta gurfanar da wadanda aka kama da safarar manyan miyagun kwayoyin a gaban shari'a, inda sauran masu shan kananan kwayoyin kuma aka kai su cibiyoyin da za a saisaita tunaninsu."

Mujallar Economic Confidential ta fitar da jadawalin yadda binciken na NDLEA ya kasance cikin shekara hudu kamar haka:

Yawan masu laifin tu'ammali da manya da kananan miyagun kwayoyi da aka kama a shiyyoyin kasar shida

LambaSHIYYA 2012 2013 2014 2015Adadi

1Arewa maso yamma 2,185 2,2882,2612,2058,939

2Kudu maso Yamma 1,5911, 9411,6821,7856,999

3Arewa ta Tsakiya 1,230 1,323 1,4161,6055,574

4Kudu maso Kudu 1,480 1,371 1,3141,3805,545

5Kudu maso Gabas 960 1,155 1,3169794,230

6Arewa maso Gabas 606 7651,0178243,212

ADADI 8,052 8,8438,8268,77834,499

Hukumar NDLEA tana yawan kama masu safarar miyagun kwayoyi a Najeriya, hakan ce ta sa shugaban hukumar ya bukaci jami'ansa da su tsaurara bincike a filayen saukar jirgin sama da ke kasar, musamman na Kaduna, da a yanzu nan ne aka fi amfani da shi a Arewacin kasar saboda rufe na Abuja da aka yi.

Wani bincike da aka gudanar ne ya gano cewa masu safarar irin wadannan kwayoyi na shirya mayar da filin jirgin Kadunan wajen dabdalarsu, a cewar NDLEA din.