Sashen Hausa na BBC ya cika shekara 60: Jiya ba yau ba

BBC Hausa ta zama gagarabadau tsakanin takwarorinta
Image caption BBC Hausa ta zama gagarabadau tsakanin takwarorinta

Bana Sashen Hausa na BBC ya cika shekara 60 da kafawa. A cikin waɗannan shekaru Sashen ya zama gagarabadau tsakanin takwarorinsa da ke watsa shirye-shirye da harshen Hausa daga ƙasashen waje.

Ya kuma cim ma haka ne ta taka rawar a zo a gani a muhimman lokuta na muhimman abubuwan da masu saurare ke so su ji.

Marigayi Aminu Abdullahi Malumfashi ne ya buɗe Sashen Hausar na BBC ranar 13 ga Maris 1957 da wani gajeren shiri na minti 15.

An ci gaba da shirin a ranakun Laraba da Jumma'a. Ranar 1 ga Yuni 1958 ne aka mayar da shirin na kullum, aka kuma ɗauki cikakkun ma'aikata.

Hausar ce harshen Afrika da aka fara buɗe wa sashe a BBC. Bayan watanni ne aka buɗe Swahili da Somali.

A ƙarshen 1958, an faɗaɗa shirin minti 15 na Sashen Hausar zuwa rana da yamma. A 1962 an ɓullo da shirin safe, minti 15, aka mayar da na rana minti 30.

Zuwa 1966 an mayar da shi ma shirin yamma minti 30. Bayan fiye da shekara 20 kuma, an mayar da shi ma na safen minti 30.

Yadda ake aikin ya sauya sosai, daga labarai da jawabi daga London da kuma wani lokaci 'yar hira da baƙon da ya je can, zuwa jin wakilai da rahotanni da suke aika wa BBCn ta waya, sai kuma wannan zamani na aikawa ta intanet.

A cikin BBCn ma an tashi daga aiki da tafureta zuwa kwamfuta da intanet.

Image caption Ma'aikatan sashen Hausa na BBC Lawal Y Saulawa da Shehu Mu'azu

A shekarar 2002 an buɗe ofis a Abuja. A 2006 kuma an mayar da Shirin Safe can, aka kuma tagwaita shi da wani shiri sabo ful, na Hantsi. Shirin Hantsin ya ba da damar samar da labaran wasanni masu yawa ga matasa.

Tun farko Sashen ya kasance majiyar shirye-shiryen ba da 'yanci ga Najeriya da sauran ƙasashe. Hira da Firmiyan Jahar Arewa, Sir Ahmadu Bello, a ziyarsa Biritaniya bayan samun 'yancin, har gobe tana jan hankalin masu saurare.

Hirar da ta ja hankali a wannan zamani, ta kawo ƙarshen rufa-rufa, ita ce wadda Sashen ya yi da jami'in sojan Najeriya, wanda ya ce sun miƙa wa 'yan-sanda Muhammadu Yusuf da ransa, wato jagoran Boko Haram.

Haka kuma hirar Sashen Hausa da Shugaba 'Yar'aduwa a lokacin da ake ta ƙila-wa-ƙala game da lafiyarsa da kuma inda yake.

Hirar A'isha Buhari ma ta ja hankalin duniya, inda ta faɗi batutuwan da wasu ke ganin tamkar kware mijinta ne baya a bainar jama'a, domin ba a ta'ba jin irin hakan ba a wannan zamani daga bakin matar wani shugaba mai ci.

Jama'a na yi wa Sashen caa a lokutan juyin mulki ko juya-hali, misali a Najeriya, da Iran da Tarayyar Sobiyat don jin ingantaccen labari da dumi-dumi.

Sanin haka ne ma ya sa a lokacin rugujewar gwamnatocin kwaminisanci a gabacin Turai, Sashen ya tura mutum can, inda ya ɗauko rahoto tare da sautin ƙwanƙwasar da masu zanga-zanga ke wa Bangon Balin, suna ƙoƙarin rusa shi.

Kuma Sashen ya zama babban fagen fafitikar kawar da mulkin soja a Jumhuriyar Nijar, abin da ya kai ga yin taron ƙasa da maida mulki hannun farar hula.

Image caption Wani tsohon ma'iakacin BBC Ambasada Adamu Muhammad yana hira da Sarudanan Sokoto

Haziƙan 'yan jarida daga wurare daban-daban sun ƙara yawa da ingancin rahotannin da jama'a ke son ji, daga Jos, Kaduna, Lagos, ko Maiduguri. BBC na cikin na farko wajen shiga Dajin Sambisa da ɗauko rahoto.

Ga kuma shirye-shirye irin su Ra'ayi Riga ko Gane Mini Hanya don tattauna muhimman batutuwa dalla-dalla, da shirye-shiryen kai tsaye daga inda talakawa suke, misali shirin BBC Hausa a Karkara, inda aka shiga lungunan arewacin Najeriya.

Akwai kuma shirye-shiryen da suka daɗe mutane na sha'awarsu irin su Amsoshin Takardunku don wayar da kai da Taɓa Kiɗi -Taɓa Karatu don ilmantarwa da nishaɗantarwa.

Akwai waɗanda suka wuce irin su Duniya Tumbin Giwa, da Kimiyya da Fasaha, da Kasuwancin Zamani, da Ilimi Gishirin Rayuwa, da Haifi Ki Yaye, da gasanni irin su Hikayata da ba a daɗe da kammalawa ba.

Da ma can Sashen ne aka fi saurare tsakanin sassan BBC in ka cire na Ingilishi da ke watsa shirye-shirye koyaushe. Zuwan intanet kuma ya ƙara bai wa Sashen Hausar damar ba da labarai ta intanet a koyaushe.

Image caption Wasu tsoffin ma'aikatan sashen Hausa na BBC

Haka shi ma sauraren shirin rediyon. Sannan ana jawo jama'ar don yin shirye-shiryen tare da su da nuna masu su kai tsaye ta kafofin sada zumunta.

Ta sashen, jama'a na samun sahihan labarai a zamanin da labaran bogi ke neman zama tuwon gandu. Haka kuma an samu damar koya wa jama'a aikin jarida da ma gyatta Hausarsu a Cibiyar Horarwa ta BBC.

Wani babban sauyin shi ne tashin BBC baki-ɗaya a 2012 daga Bush House zuwa New Broadcasting House, ginin gilashi mai cike da na'urori na zamani.

A ranar 30 ga Yuni 2012 ne Sashen ya soma watsa shirye-shiryensa a wannan sabon gini.

Ma'aikan Sashen Hausar na BBC kuma, waɗanda duk nasarar nan da aka samu su ne suka samar da ita, ba su ga ta zama ba wajen tabbatar da Sashen ya ci gaba da tsere sa'a.

A yau intanet da sauran hanyoyi na dijita sun bai wa kowa damar watsa labarai cikin sauƙi.

Don haka, wannan sabuwar gogayya ce wadda yanzu ne aka fara ta.