Nigeria: Za a kare masu fallasa manyan barayi

Hakkin mallakar hoto EFCC
Image caption Ana zargin manyan mutane da sace makudaden kudade da ya kamata a yi amfani da su wajen bunkasa Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta jaddada aniyarta ta bai wa masu tsegunta inda aka boye kudaden sata a kasar cikakkiyar kariya, a ci gaba da kokarin da ta ke yi na yaki da matsalar cin hanci da rashawa.

Gwamnatin ta ce kara bai wa 'yan kasar tabbacin kariyar ya zamo wajibi saboda da fargabar da wasu ke nunawa cewa idan suka fallasa manyan barayi na gwamnati ko na kamfanoni, ba za su samu kariya daga cin zarafi na manyan mutanen da suka fallasa ba.

A kwanakin baya ne dai gwamnatin ta Najeriya ta bullo da wata dabara ta yaki da cin hanci da rashawa, inda ta yi alkawarin bai wa duk wanda ya fallasa inda aka boye dukiyar sata wani tukwici daga cikin abin da aka kwato na kudaden, lamarin da ya kai ga gwamnatin kasar ta samu gano makudadan kudade da aka boye, wadanda ake zargin na sata ne.

Ministan Watsa Labarai da Raya Al'adu na kasar, Alhaji Lai Mohammed, ya ce Kwamitin Karbo Dukiyar Gwamnati na Fadar Shugaban Kasa, ya samu bayanai daga daidaikun 'yan Najeriya da kungiyoyi wadanda suka nuna fargaba kan tsaron lafiyar masu fallasa wadanda ake zargin manyan barayi ne da suka sace dukiyar gwamnati suka boye.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Minista Lai Mohammed ya ce za a kare masu kwarmata manyan barayi domin su samu kwarin gwiwar ci gaba da fallasa.

To amma minsitan ya kara da cewa ''Kada masu fallasa su ji tsoro, domin kwamitin ya tanadi matakai na kare wadanda suka bayar da muhimman bayanai. Hasali ma, masu fallasa za su more, ba za su yi hasara ba''.

Cikin wata sanarwa da mataimakinsa na musamman, Segun Adeyemi, ya sanya wa hannu, ministan ya kara jaddada alkawarin da gwamnati ta yi na cewa duk wanda ya tsegunta maboyar dukiyar haramun, kuma aka kai ga karbo dukiyar, to za a ba shi ladan fallasa kuma ba za a bayyana shi ko kuma sunansa ba.

Minista Lai Mohammed ya ce wanda ya fallasa inda aka boye kudin da ya kai Naira biliyan daya, to za a ba shi kashi biyar cikin dari na kudin. Wanda ya fallasa kudin da suka fi Naira biliyan daya kuma, za a ba shi kashi biyar cikin dari na Naira biliyan dayar, sannan kuma a ba shi kashi hudu cikin dari na sauran kudin da suka zarta Naira biliyan daya.

Image caption Yaki da cin hanci da rashawa na daya daga cikin manyan manufofin gwamnatin Nijeriya

A cewar Alhaji Lai Mohammed, idan kudin da aka gano kuma sun wuce Naira biliyan biyar, to za a bai wa wanda ya tsegunta maboyar kudin kashi biyu da rabi cikin dari na kudin, bayan an ba shi kashi biyar cikin dari na Naira biliyan daya ta farko, da kuma kashi hudu cikin dari na Naira biliyan hudu.

To sai dai kuma Ministan na watsa labarai bai bayyana adadin kudade da gwamnatin ta samu ba kawo yanzu tun bayan bullo da wannan sabon tsari na bai wa masu fallasa tukwici a yunkurin yaki da matsalar ta cin hanci da rashawa a watan Disamba da ya gabata.

Matsalar cin hanci da rashawa, a cewar masharhanta, ta yi wa Najeriya katutu tare da tauye ci gabanta cikin shekaru da dama.