'Mu muka fito da London take kira a BBC Hausa'

Adamu Muhammad yana hira da Sardunan Sokoto a Ingila
Image caption Adamu Muhammad yana hira da Sardaunan Sokoto a Ingila

Ɗaya daga cikin mutum uku da suka buɗe sashen Hausa na BBC ya ce yana jin daɗi ganin gidan rediyon da suka fara aiki, ba kawai bunƙasa yake yi ba, yana ma faɗaɗa harshen Hausa.

Alhaji Adamu Muhammad ya ce shi ne mutum na uku da aka ɗauka aiki a sashen Hausa na BBC bayan marigayi Balarabe Fatika da Umaru Dikko.

Ya ce ya yi aiki da BBC Hausa daga shekarar 1957 zuwa 1962 kuma a lokacin babu ci gaban da aka samu kamar yanzu ta fuskar kayan aiki da yawan ma'aikata.

Ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi, a wani ɓangare na bikin cikar Sashen Hausa na BBC shekara 60 da kafuwa.

A cewar shugaban sashen, Jimeh Saleh BBC Hausa zai shafe kwana 10 yana gabatar da shirye-shirye na musammam kan wannan dogon zango da aka cim ma.

A tsawon kwanakin, BBC Hausa zai gabatar da rahotanni da hirarraki da tsoffin ma'aikatansa da kuma na yanzu gami da masu sauraron tashar tun tale-tale da kuma matasa.

Adamu Muhammad dai ya ce sun fara aiki ne su uku, kafin a ƙaro ma'aikata irinsu Ahmed Yakubu da Musa Musawa da Aminu Tijjani (Turakin Zazzau) da Ibrahim Tahir..

Ma'aikacin farko na Sashen Hausa na BBC, ya ce su ne suka fito da fitaccen taken buɗe shirin BBC Hausa na "London take kira, Sashen Hausa na BBC ke magana".

A cewarsa fassara suka yi daga Ingilishi, inda ake cewa "London's calling, BBC is speaking."

Adamu Muhammad wanda shi ne kaɗai cikin mutum ukun da suka gabatar da shirye-shiryen BBC Hausa da yake raye, ya ce sun fara ne da gabatar da labarai sau biyu a rana.

Labarai masu alaka