Idan ka ji labari daga BBC to ka ji ƙurewarsa - Prof Ayagi

Farfesa Ayagi
Image caption Farfesa Ayagi ya yi aiki da BBC daga shekarar 1964 zuwa 1967

Wani tsohon ma'aikacin BBC, Farfesa Ibrahim Ayagi ya ce BBC (Sashen Hausa) ake zuwa don jin sahihan labarai na gaskiya a ko da yaushe.

Farfesa Ibrahim Ayagi wanda ya yi aiki da Sashen Hausa na BBC tsawon shekara uku daga 1964 zuwa 1967 ya ce matuƙar labaran gaskiya ake son ji da tsagwaron labarai, to sai BBC.

Ibrahim Ayagi ya ce "Idan ka ji labari daga BBC to ka ji ƙurewarsa, shi ne gaskiya. Shi ne abin da kake buƙata, in dai gaskiya kake buƙata."

Tsohon ma'aikacin na BBC Hausan ya bayyana haka ne a wani ɓangare na bikin cikar Sashen Hausa na BBC shekara 60 da kafuwa.

Masanin tattalin arziƙin ya ce shi daɗaɗɗen mai sauraron BBC ne kuma yana da burin ci gaba da karatun jami'a bayan kammala karatunsa na kwalejin koyon aikin malanta.

Ya ce ya nemi aiki da BBC don ya samu damar ƙara karatun da zai ba shi damar shiga jami'a kuma ba zato ba tsammani sai BBC ta aiko masa cewa ta ɗauke shi aiki.

Tsohon mashawarcin shugaban Nijeriyar kan fannin tattalin arziƙi ya ce ya riƙa yin aiki da BBC London a lokaci guda yana karatu, inda ya dinga tsimin abin da yake samu a asusun ajiya yana aikowa gida.

Ya ce ai ka san BBC har yanzu, a wajena idan ka saba da BBC, shi kenan ka saba da BBC to ba kuma wata kafar labarai sai BBC.

A cewarsa tun suna nan haka aka nuna musu cewa labarai daban, ra'ayi daban, kuma ra'ayi ba ya shiga cikin labarai lallai ya zama yadda ka same shi haka za ka bayar, ba za ka sa masa wani abu da zai sauya masa salo ba.

"Haka suka tsara (Sashen) Hausa ɗin kuma haka zai tafi insha Allahu"

Labarai masu alaka