Ɗaurarru na bore a kan hana su dafa abinci

Guatemalan Prison Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu sun so yin amfani da wannan damar don su tsere

'Yan sanda sun ce an kashe jami'in tsaro biyu a wani bore da ya ɓarke a cibiyar tsare fanɗararrun matasa da ke ƙasar Guatemala.

An kuma jikkata ƙarin biyar waɗanda fursunonin suka yi garkuwa da su a cibiyar Etapa II a birnin Guatemala.

Ɗaurarrun na buƙatar a ba su dama su riƙa karɓar ɗaurin abinci daga waje kuma a ba su izinin dafa abincinsu da kansu.

'Yan sandan kwantar da tarzoma sun kewaye gidan yari har ma sun harba hayaƙi mai sa hawaye amma dai sun gaza ƙwace iko da cibiyar a kan lokaci.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sanda kafa shinge a katangar gidan yarin

Fursunonin sun cinna wa katifunsu wuta kuma wasu sun hau kan rufin cibiyar, yayin da wasu suka yi ƙoƙarin arcewa.

Jami'ai sun ce gungun wasu tsageru ne da ake kira 18th Street Gang suka tayar da hargitsin.

Daga cikin buƙatunsu akwai cewa a mayar da takwarorin gungunsu da ke wasu gidajen yari zuwa Etapa II.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Har duhun dare ya sauka 'yan sanda ba su iya shawo kan boren ba

Shaidu sun ce ɗaurarru 'yan gungun 18th Street sun kuma yi barazanar kashe abokan hamayyarsu na gungun Paisas matuƙar suka ƙi shiga boren.

Wakilan gungun tsageru 'yan tarzoma a kan tituna na da tarin yawa a gidajen yarin Guatemala, inda ake yawan samun munanan rikice-rikice.

Lamarin ya zo ne ƙasa da mako biyu bayan mutuwar 'yan mata 40 a wata gobara da ta tashi a wani gidan kula da yara na gwamnati a kusa da birnin Guatemala.

Labarai masu alaka