Kotun ICC za ta yankewa Bemba hukunci

MLC ta zamo jam'iyyar siyasa daga baya
Image caption Jean Pierre Bemba Gombo ya jagoranci gungun 'yan tawaye mai suna MLC

A ranar Laraba ne tsohon mataimakin shugaban Congo, Jean-Pierre Bemba Gombo zai sake gurfana a gaban Kotun Manyan Laifuka ta duniya wato ICC, kan bayar da toshiyar hanci ga shaidu.

Daman dai a yanzu haka mista Memba yana daure a gidan yari har na tsawon shekara 18 bisa laifukan yaki da na cin zarafin al'umma.

A bara ne kuma aka kama shi tare da wasu abokansa guda hudu da laifin ba wa shaidu toshiyar baki da kuma jirkita shaida a shari'ar da ake yi masa ta laifukan na yaki.

Kotun dai ta samu labarin cewa mista Bemba ya hada wata kungiya ta masu bai wa shaidun da suke da bayani kan laifukan yakin da ake tuhumar sa da su, toshiyar baki domin su ki fadar gaskiya.

'Yan kungiyar tasa dai sun yi amfani da waya a asirce da kuma wasu yarukan da su kadai ke iya fahimta wajen hana shaidu guda 14 bayar da bahasin abun da suka sani a kan mista Bemba.

An dai samu lauyan mista Bemba wanda abokin siyasarsa ne da kuma wani mai bada shaida guda da laifuka fiye da 100.

Kuma suna fuskantar hukuncin daurin shekara 5 a gidan yari ko tara ko kuma a hade hukuncin baki daya.

Wannan dai shi ne karon farko da ake sauraron shari'ar da ta jibanci rashawa da cin hanci, a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC.

Kotun ta ICC dai na fatan shari'ar ta mista Bemba za ta zama darasi ga masu sha'awar kawo cikas ga shari'a ta hanyar bayar da cin hanci.