Dole mu yaki ta'addanci — Le Pen

Akwai dakarun Faransa da dama a Chadi wadanda ke yaki da 'yan ta'adda Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akwai dakarun Faransa da dama a Chadi wadanda ke yaki da 'yan ta'adda

'Yar takarar shugabancin kasar Faransa Marine Le Pen ta gudanar da wata tattauanawa da shugaban kasar Chadi Idris Deby Itno.

Marine Le Pen ta bayyana tattaunawar ta su a matsayin wani yunkuri na yaki da ta'addanci.

'Yar takarar shugancin kasar ta Faransa ta ziyarci Chadi ne domin samun damar ganawa da wasu daga cikin dakarun kasarta dubu hudu wadanda ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar.

Sojoji da dama sun rasa rayukansu a Chadi a yayin da suke yaki da 'yan kungiyar Al Qaeda.

Ms Le Pen ta ce a matsayinta na shugabar kasa za ta duba hanyoyin da zasu kara karfafa dangantaka tsaro a tsakanin kasashen biyu.

Labarai masu alaka