Majalisar Dattawan Nigeria ta nemi Hameed Ali ya yi murabus

Bukola Saraki
Image caption An zargi shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki da sayen wata mota gagara-harsashi

'Yan majalisar dattawan Najeriya sun bukaci shugaban hukumar fasa kwauri, Kanar Hameed Ali mai ritaya ya sauka daga kan mukaminsa saboda kin sanya kakin hukumar.

'Yan majalisar sun ce Hameed Ali bai cancanta ya ci gaba da zama kan mukamin gwamnati ba .

Sun dauki matakin ne saboda shawarar da shugaban hukumar ta fasa kwauri ya yanke ta kin bayyana a gaban su ranar Laraba, kamar yadda suka bukaci ya yi.

Hameed Ali ya shaida wa manema labarai ranar Talata cewa ba zai bayyana a gaban majalisar ba saboda shawarar da aka ba shi cewa kada ya yi hakan saboda wani ya shigar da kara a kotu inda ya nemi ta fassara masa jalasci ko akasin hakan na sanya kakin hukumar ga shugabanta.

'Yan majalisar dattawan da shugaban hukumar fasa kwaurin sun soma takun-saka ne bayan da hukumar ta bayyana cewa za ta fara kama duk mai motar da ba shi da takardar da ke nuna cewa ya biya kudin futo.

Batun dai ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin 'yan kasar, lamarin da ya sa hukumar ta dakatar da shi amma duk da haka majalisar dattawan ta nace cewa dole Hameed Ali ya bayyana a gaban ta sanye da kakin hukumar don ya yi mata bayani kan batun.

Masu sharhi dai na ganin wannan takaddama ta dauki sabon salo ne saboda zargin da ake yi wa shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki da sayen wata mota gagara-harsashi, wacce hukumar ta fasa kwauri ta kwace.

Sai dai Mr Saraki ya ce motar ta majalisar dattawa ce ba ta sa ba ce.

Labarai masu alaka