Kalmomin da aka fara amfani da su a BBC Hausa
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Saurari kalmomin da aka fara amfani da su a BBC Hausa

Wani tsohon ma'aikacin Sashen Hausa na BBC, Zakari Mohammed ya bayyana wasu daga cikin kalmomin farko da aka fara amfani da su a sashen, wanda aka kafa shekara 60 da ta wuce.

Ya ce shirye-shiryen Sashen na farko sun fi mayar da hankali kan abubuwan ban sha'awa na mutanen Ingila da sauran rayuwar Turawa.

Malam Zakari Mohammed ya ce ya fara aiki da Sashen Hausa na BBC ne bayan ya halarci bikin samun 'yancin kan ƙasar Ghana, lokacin da yake karatu a London, inda ya buƙaci a ba shi dama ya gabatar.

Labarai masu alaka