IS ta ɗauki alhakin harin Burtaniya

Wurin da aka kai harin Landan Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ma'aikatan agaji sun kai har yamma suna aikinsu a wurin da lamarin ya faru

Kungiyar IS da ke ikirarin kishin Musulinci ta ce ita ta kai hari a majalisar dokokin Burtaniya ranar Laraba, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutum hudu, ciki har da maharin.

Kungiyar ta bayyana a wani kamfanin dillancin labaranta cewa mutumin da ya kai harin "sojin kungiyar Islamic State ne".

Ita kuwa Firai Ministar Burtaniya Theresa May ta ce maharin haifafen kasar ne wanda kuma 'yan sanda da jami'an leken asiri suna sane da shi.

A wata sanarwa da ta aike wa majalisar dokoki Ms May ta ce an taba gudanar da bincike kan mutumin a wasu shekaru da suka wuce a kan ta'addanci.

An kama mutum takwas a London da Birmingham bisa zargin hannu a kai harin.

Hakkin mallakar hoto PA/FACEBOOK
Image caption PC Keith Palmer da Aysha Frade na cikin wadanda suka mutu

Mutanen da suka mutu sanadin harin sun hada da: PC Keith Palmer, Aysha Frade, wacce ke aiki a kwalejin birnin London da kuma wani mutum mai kimanin shekara 50.

Bakwai daga cikin mutanen da suka jikkata na kwance a asibiti magashiyan.

Sai dai 'yan sanda sun ce an bai wa wasu mutum 29 magani, sannan aka sallame su.

'Duniya na alhini'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutane a Brussels sun nuna alamar zuciya da hannayensu domin tuna harin da aka kai a Belgium a bara

Shugabannin kasashen duniya wadanda suka fuskanci hare-haren ta'addanci a baya-bayan nan sun yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai a majalisar wakilan Burtaniya.

Shugabannin kasashen Faransa da Jamus, wadanda suka fuskanci hare-haren motoci a shekarar da ta gabata, sun nuna goyon bayansu ga kasar Burtaniya.

Shugaban Amurka ya mika sakon ta'aziyyarsa ga kasar, ya kuma yaba wa jami'an tsaron Burtaniyar.

Daga cikin wadanda suka raunata a kan gadar masu tafiya a kasa ta Westminster, akwai yara uku 'yan makaranta 'yan asalin kasar Faransa, da 'yan Romaniya biyu. Haka kuma akwai 'yan Koriya ta kudu biyar da suka samu rauni a hargitsin da ya biyo bayan harin.

A birnin Faris, an kashe wutar hasumiyar Eiffel Tower da tsakar dare, domin nuna alhininsu ga wadanda lamarin ya shafa.

Shugaba Francois Hollande ya nuna goyon bayansa ga mutanen Burtaniya, inda ya ce "ta'addanci abu ne da ya shafe mu gaba daya, kuma Faransawa sun ji yadda 'yan Burtaniya suka ji yau."

Labarai masu alaka