Dino Melaye ya nemi Sahara Reporters ta ba shi $16m kan bata suna

Sanata Dino ya ce yana so hakan ya zama izina
Image caption Sanata Dino ya ce yana so hakan ya zama izina

Wani fitaccen dan majalisar dattawan Najeriya Dino Melaye ya kai karar jaridar Sahara Reporters a gaban kotu kan bata masa suna inda ya bukaci ta biya shi diyyar $16m.

Jaridar dai ta wallafa wani labari da ke cewa dan majalisar dattawan ya yi karya wajen kammala digirinsa, tana mai cewa ba shi da shaidar digiri ta Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria da kuma Jami'ar Harvard da ke Amurka.

Sai dai a takardar karar da ya shigar, Sanata Melaye ya ce ya kammala digirinsa na farko a Jami'ar Ahmadu Bello a shekarar 1999, inda ya fita da digiri na mataki na hudu.

Dan majalisar, wanda ke wakiltar Kogi ta yamma a jam'iyyar APC, ya kuma wallafa hotonsa tare da wasu daliban da suka yi wa kasa hidima bayan kammala karatun digirinsa na farko.

A cewarsa, ya kai Sahara Reporters kotu ne domin hakan ya zama izina ga jaridun da ke bata sunan mutane musamman 'yan siyasa kamarsa.

Ba wannan ne karon farko da ake sa'insa tsakanin Sahara Reporters da Sanata Melaye ba.

A kwanakin baya ma jaridar ta wallafa wasu takardu da tace sun nuna yadda sanatan ya mallaki asusun banki a Amurka ba bisa ka'ida ba, zargin da Mista Melaye ya musanta.

Labarai masu alaka