Nigeria ta kashe $2.6 bn kan Boko Haram a 2016

Janar Abayomi Olonisakin (na farko daga dama) tare da hafsoshin rundunonin sojin Najeriya Hakkin mallakar hoto Nigeria government
Image caption Janar Abayomi Olonisakin (na farko daga dama) ya ce za su murkushe ta'addanci

Babban Hafsan Dakarun Tsaron Najeriya ya ce kasar ta kashe fiye da dala biliyan biyu da miliyan dari shida a shekarar 2016 kawai domin bayar da agaji ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa.

Janar Abayomi Olonisakin ya bayyana haka ne a wurin wani taro da aka yi a birnin Washington na Amurka a kan gamayyar da ake yi wajen murkushe kungiyar IS.

A cewarsa, "Duk da kashe fiye da dala biliyan biyu da miliyan dari shida da gwamnatin Najeriya ta yi a 2016 domin bayar da agaji ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa, har yanzu akwai bukatar bayar da tallafi, musamman bayan an sake kwato garuruwan da ke hannun 'yan kungiyar."

Makiyin duniya

"Yawancinku da ke wannan dakin sun zo taron da muka yi a Oslo babban birnin kasar Norway a watan Fabrairu domin nuna goyon bayansu ga Najeriya. Hadin gwiwa na da matukar muhimmanci. Don haka muna gode wa Sakatare Rex Tillerson da Shugaba Donald Trump saboda jajircewarsu ta yaki da makiyin duniya - ta'addanci."

Ya kara da cewa yakin da kasar Iraki ke yi da kungiyar IS irinsa Najeriya ke yi da Boko Haram.

Ci gaba

Janar Olonisakin ya bayyana cewa a shirye Najeriya take ta hada kai da sauran kasashen duniya domin kawar da ta'addanci.

Ya kuma yaba da ci gaban da aka samu a Iraki da Syria na hana wa kungiyar IS damar kwace wasu yankuna da kuma katse hanyoyin samun kayan aiki.