Zagon kasa jam'iyyun adawa ke mana- PNDS

Jam'iyyar PNDS mai mulki a Nijar ta ce jam'iyyun adawa ne suka jefa kasar cikin halin da ta ke ciki Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jam'iyyar PNDS mai mulki a Nijar ta ce jam'iyyun adawa ne suka jefa kasar cikin halin da ta ke ciki

A jamhuriyar Nijar, jam'iyar PNDS mai mulki ta zargi kawancen jami'iyyun adawar kasar da yunkurin yi wa gwamnatin shugaba Muhammadu Issoufou zagon kasa.

A cikin wata sanarwar da ta fitar jiya Laraba, jam'iyyar ta ce 'yan adawar sun dukufa wajen yada farfagandar karya kan mulkin Shugaba Issoufou da manufar durkusar da gwamnatinsa.

PNDS ta ce 'yan adawa ne suka janyo halin da Nijar din ta tsinci kanta, kuma suna hakan ne dan su barar da gwamnati mai ci.

To sai dai kuma shugaban jam'iyyar adawa ta Model Lumana na wucin gadi,Umaru Noma ya ce idan mafadin magana wawa ne, ai yakamata mai sauraro ya yi hankali, abinda ake zargin kawancen jam'iyyun adawa da aikatawa ba haka bane, kuma ai al'ummar kasar na ganin komai da idanunsu.

Masana kan al'amuran siyasa a kasar dai na cewa, kasar ta kama wata hanya da sai dai gyaran Allah kawai.

A watannin baya dai 'yan adawar sun sha yi gangamin kin jinin gwamnati a sassan kasar daban-daban tare da yin kira ga shugaban da ya sauka, koda yake sun musanta wannan zargin.

Labarai masu alaka