Ana fargabar nutsewar mutum 200 a gabar tekun Libya

Dubban 'yanci rani na rasa rayukansu a yayin da suke kokarin tsallakawa Turai Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dubban 'yanci rani na rasa rayukansu a yayin da suke kokarin tsallakawa Turai

Wata kungiyar agaji ta kasar Spaniya ta ce akwai fargabar cewa 'yan cin rani 200 sun mutu bayan da wasu kwale-kwale 2 suka nitse a gabar tekun Libya.

Kungiyar mai suna Proactiva Open Arms, ta ce ya zuwa yanzu an gano gawawwaki biyar suna yawo a kusa da kwale-kwalen biyu da suka kife, wanda kowannensu ke dauke da mutum dari- dari.

Kungiyar ta ce mutanen da aka ganon dai matasa ne wanda da alama sun nitse ne.

Wani mai magana da yawun masu tsaron tekun Italiya ya tabbatar da mutuwar mutanen biyar.

Sai dai kuma ya shaidawa BBC cewa ba za su iya tabbatar da adadin mutanen da suka mutu wanda kungiyar ta bayar ba.

Kungiyar dai ta ce akalla 'yanci rani dari biyu da arba'in sun mutu, saboda yadda mutane suka yiwa kwale-kwalen yawa.

Ana samun karuwar 'yanci ranin da ke kokarin isa nahiyar turai daga Libya.

Hukumar da ke kula da 'yanci rani ta kasa da kasa ta ce fiye da 'yanci rani dubu ashirin sun isa Italiya a cikin shekarar da muke ciki, yayinda aka kiyasta cewa wasu dari biyar da hamsin da tara kuma ko sun mutu ko kuma sun bata a kan hanyarsu ta zuwa turan.

Labarai masu alaka