Kudurin Trump kan lafiya na fuskantar cikas

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shirin kiwon lafiya na Obamacare ya samawa Amurkawa miliyan 20 ingantaccen shirin kiwon lafiya mai rahusa

Shugaban Amurka, Donald Trump ya bukaci da a dakatar da kada kuri'a da majalisar dokoki ke yi a jiya Alhamis, na yi wa tsarin kiwon lafiyar tsohon shugaban kasar, Barack Obama garanbawul.

Hakan dai ya faru ne saboda shakkun da mista Trump ke da shi na samun isasshen goyan bayan da zai iya sanya kudirin ya zama doka.

An dai dade ana kai ruwa-rana wajen amincewa da kudirin amma al'amarin ya ci tura abin da ya janyo mista Trump sanya yau Juma'a ta zama ranar karshe kan kudirin.

'Yan majalisar dokoki daga jam'iyyar Mr Trump da dama , sun yi barazanar kin amincewa da dokar, matukar ba a yi wasu 'yan sauye-sauye a cikinta ba.

Wannan dai zai zama kamar wata 'yar manuniya ga nasara ko akasinta da gwamnatin shugaba Trump za ta yi musamman dangane da alkawuran da ya yi lokacin yakin neman zabe.

Kudiri yiwa tsarin inshorar lafiyar na Obamacare garanbawul na bukatar amincewar 'yan majalisar 215, to sai dai ya fara samun cikas daga 'yan jam'iyyar Republican masu ra'ayin mazan jiya, saboda a cewarsu sabon tsarin na neman gusar da tsohon tsarin.

Shi dai shirin kiwon lafiya na Obamacare ya samawa Amurkawa miliyan 20 ingantaccen shirin kiwon lafiya mai rahusa da a baya ba su san ana yi ba.

Shi kuma mista Trump ya na son maye gurbin wancan tsari da mafi rahusa wanda mutanen kasar miliyan 24 za su amfana daga yanzu zuwa 2026.

Labarai masu alaka