Nigeria: Za a hukunta marasa na'urar takaita gudun motoci

Image caption Kashi casa'in cikin dari na hadurran da ake samu a kan titunan Najeriya, gudun ke ta sa'a ke janyo shi

Hukumar kiyayye afkuwar hadurra ta Najeriya wato FRSC, ta ce ta fara hukunta direbobin motocin hayar da basu sanya na'urar takaita gudun motoci da aka bullo da ita a kasar ba.

Hukumar ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa kashi casa'in cikin dari na hadurran da ake samu a kasar, na faruwa ne sakamakon yawan gudu da direbobi motoci ke yi a kan hanyoyi.

Hukumar ta ce an samu gagarumin cigaba tun bayan da aka bullo da na'urar, domin kuwa tun daga ranar 1 ga watan Fabrairu shekarar da ake ciki, dokar hukunta wanda bashi da na'urar a motarsa ta fara aiki, musamman masu motocin haya.

Wani jami'ai a hukumar, Muhammad Kabir Abubakar ya yi watsi da zargin da wasu ke yi cewa na'urar na lalata injin mota, in da ya ce sai da aka kai na'urar hukumar kare hakkin masu amfani da kaya ta tantance ingancin na'urar, kafin aka bada umarnin a fara amfani da ita.

Jami'in ya kuma ce,kamar yadda masu motoci musamman na haya ke korafin cewa a'urar na da tsada, sam ba haka bane, an sanya farashinta ne a kan yadda mutane za su iya saya.

Muhammad Kabir Abubakar, ya ce dokar sanya na'urar takaita gudun motocin ba wai a kan masu motar haya kadai ta tsaya ba, har ma da masu motocin kansu.

Dan haka wajibi ne kowa ya saka na'urar a motarsa, dan gudun kada hukuncin rashin sanya ta ya hau kansa.

Jami'in ya ce yakamata mutane su gane cewa, an samar da wannan na'ura ne domin rage yawan hadurran da ake samu a kan titunan Najeriya baki daya.

Labarai masu alaka