'Yan Republican ne suka kawo wa kudirina cikas —Trump

Mr Trump ya ce bai ga laifin kowa ba illa 'yan jam'iyyarsa ta Republican dan su suka janyo kudirin nasa ya samu cikas Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Trump ya ce bai ga laifin kowa ba illa 'yan jam'iyyarsa ta Republican dan su suka janyo kudirin nasa ya samu cikas

A karon farko shugaba Trump ya gamu da cikas a kudurin dokarsa ta farko tun bayan da ya hau mulki.

'Yan majalisar dokokin kasar sun ajiye kudirin a gefe ne sakamakon kasa samun yawan kuri'ar da ta dace domin zama doka.

Kuma hakan ya faru ne saboda wasu daga cikin 'yan majalisar jam'iyyar republican ta shugaba Donald Trump ba su gamsu da kudirin dokar ba.

Maye gurbin shirin inshorar lafiya ta Obamacare shi ne babban alkawarin da Mr Trump ya yi a lokacin yakin neman zabe.

Shugaban na Amurka ya ce ya yi mamaki kwarai da gaske da wannan sakamako in da ya ce bai ga laifin kowa ba illa 'yan jam'iyyarsa ta Republican wadanda su ne suka janyo kudirin nasa na yi wa dokar tsarin kiwon lafiyar kasar garanbawul, ya samu cikas.

To sai dai kakakin majalisar wakilai, Paul Ryan ya ce shi ne ya ba wa shugaba Trump shawarar a janye kudirin saboda bai samu goyon bayan da ya kamata ba a majalisar sakamakon rashin farin jini a tsakanin 'yan majalisar

Rahotanni dai sun ce 'yan jam'iyyar mista Trump 28 zuwa 35 ne suka nuna rashin amincewarsu da kudirin.

An dai ce wasu na ganin kudirin ya zabtare rahusar da tsarin kiwon lafiyar shugaba Obama ke bayarwa, a inda wasu ke kallon kudirin da gazawa wajen kawo sauye-sauye masu yawa ga tsohon tsarin.

Ana dai ganin janye kudirin daga majalisa saboda rashin farin jininsa, wata 'yar manuniya ce ga alkiblar da alakar shugaban da majalisar za ta dosa.

Shugabar jam'iyyar Democrat a majalisar wakilan kasar, Nancy Pelosi ta bayyana wannan mataki a matsayin wata babbar nasara ga al'ummar Amurka.

Labarai masu alaka