Shin hada-hada za ta dore a filin jirgi na Kaduna?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Filin jirgin sama na Kaduna ya fara morewa amma wa'adi na karatowa

Tun bayan da hukumomin Nijeriya suka dauki matakin rufe filin jirgin sama dake Abuja babban birnin kasar domin bayar da damar gudanar da gyare-gyare ga titin jirgi a filin, hada-hada ta kankama a filin jirgin sama na birnin Kaduna a wani abu mai kama da karin maganar nan dake cewa faduwar wani tashin wani.

Yanzu dai jihar ta Kaduna ta fara ganin alfanun tashi da saukar jirage dake zirga-zirga tsakanin kasa da kasa da kuma na cikin gida, a filin jirgin na Kaduna kimanin makwanni uku da suka gabata.

Yayin da wa'adin makwanni shida da hukumomin Nijeriya suka tsayar na kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama su koma filin jirgin sama na Abuja domin ci gaba da hada-hada yadda suka saba ya fara karatowa, tambayar da mutane da dama ke yi ita ce, shin yaya makomar filin jirgin sama na Kaduna zata kasance idan hada-hada ta sake komawa filin jirgin sama na Abuja ganin tuni Kaduna ta fara dandana dadin tashi da saukar jirage na kasa da kasa? Wani kokari hukumomi ke yi domin ganin filin na Kaduna bai koma gidan jiya ba?

Babban Sakataren Hukumar Zuba Jari ta Jihar Kaduna, Alhaji Gambo Hamza, ya ce yanzu haka ma'aikata kimanin dari tara ne ke aiki a filin jirgin saman na Kaduna baya ga manya da kananan 'yan kasuwa masu zaman kansu, da kuma otel-otel da harkokinsu suka kara bunkasa a sanadiyyar mayar da zirga-zirgar zuwa Kaduna.

Ya ce suna ta kokarin shawo kan kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na kasa da kasa don su kara maida harkokinsu filin na Kaduna ko da bayan an sake bude filin jirgin sama na Abuja.

Shi ma dai ministan zirga-zirgar jiragen sama na Najeriya, Alhaji Hadi Sirika, ya ce kwalli ta biya kudin sabulu game da karkatar da harkokin jirgaen saman zuwa Kaduna duk da tirjiyar da wasu suka nuna da farko.

Ga rahoton Nurah Mohammed Ringim kan halin da ake ciki:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Shin hada-hada zata dore a filin jirgin sama na Kaduna?

A farkon wannan wata ne dai aka rufe filin jirgin saman na Abuja domin a gudanar da aikin gyara titin jirgi wanda ya lalace matuka, kuma hukumomi sun ce za a kwashe makwanni shida kafin a sake bude filin jirgin na Abuja, yayin da a tsawon lokacin jirage da ya kamata su tashi ko sauka a Abuja, za su rika yin hakan a filin jirgin sama na Kaduna, wanda kafin daukar wannan mataki ba a cika jin duroiyarsa ba idan aka kwatanta shi da filaye da ke wasu manyan birane a kasar. A halin yanzu dai an kara inganta filin jirgin na Kaduna domin fitar kunya.