An yi wa Polio taron-dangi a Afirka

Polio
Bayanan hoto,

Ana yi wa yara muliyan 100 'yan kasa da shekaru biyar rigakafin Shan Inna

An kaddamar da wani gagarumin aikin rigakafin cutar Shan Inna wato Polio a Najeriya da wasu sassa na Afirka.

Ma'aikatan kiwon lafiya za su yi wa yara fiye da muliyan 100 rigakafi a Yammaci da Taskiyar Afirka a wani yunkuri na shawo kan bazuwar cutar bayan da aka samu barkewarta a arewa maso gabashin Najeriya mai fama da bala'in rikicin Boko Haram.

A Najeriya dai ma'aikatan rigakafin za su bi gida-gida, da masallatai da majami'u da kasuwanni da sauran wurare da za a iya samun yara da ba su wuce shekara biyar da haihuwa ba.

Jami'an Shirin Kawar da Cutar Polio a Duniya na cewa za a yi aikin rigakafin a kasashe goma sha uku a nahiyar Afirka. Za a yi kwanaki hudu ana aikin rigakafin.

Bayan da aka yi tsammanin an kawar da cutar ta Shan Inna a Afirka inda aka yi shekaru biyu ba a samu yaron da ya kamu da kwayar cutar ba , sai kwatsam aka bada labarin sake bullarta a Najeriya a bara.

Yara hudu ne aka samu suna dauke da kwayar cutar a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

To sai dai tun daga lokacin aka fara yunkurin rigakafi zagaye-zagye, kuma wannan shi ne zagaye na karshe wanda ya hada kasashen Afirka da dama.

Kwamishinan lafiya a jihar ta Borno, Dokta Haruna Mshelia, ya shaida wa Ishaq Khalid ta wayar tarho cewa aikin yana gudana yadda aka tsara.

Saurari karin bayani a hirarsu:

Bayanan sauti

Polio na nakasa kananan yara a duniya a cewar WHO

Ayyukan tarzoma na Boko Haram sun tarwatsa dimbin mutane, abinda ya haifar da fargabar cewa cutar za ta iya yaduwa zuwa makwabtan kasashe da ma nahiyar baki daya.

A duniya baki daya, kasashe uku ne ake da cutar a halin yanzu, wato kasashen Najeriya da Afghanistan da Pakistan a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO.