Dan siyasar Birtaniya ya sauya sheka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mista Doughglas Carswell ya yi tazarce ne a kujerarsa ta majalisa a 2015

Jam'iyyar UKIP a Birtaniya ta yi hasarar dan majalisa daya tilo da aka zaba a karkashin inuwarta inda ya fice daga cikinta.Dan majalisar wakilai Doughlas Carswell, ya ce yanzu zai zama dan majalisa mai zaman kansa wato dan Indifanda ba tare da alakanta kansa da wata jam'iyyar siyasa ba.

Jam'iyyar UKIP dai na adawa da kungiyar Tarayyar Turai, da kuma kasancewar Birtaniya a cikin kungiyar.

Wasu masharhanta na ganin ficewar dan majalisar daga cikin jam'iyyar wata alama ce ta irin rarrabuwa dake cikinta.

Dama dai jam'iyyar tana fama da rigingimun cikin gida musamman kokarin nuna iko tsakanin gaggan 'ya'yanta.

Tun farko dama dan majalisar a jam'iyyar Conservatives ya ke, amma a shekarar 2014 sai ya sauya sheka ya shiga jam'iyyar UKIP wadda ta taka rawar gani a yawan kuri'a a zabukan 2015, fiye da shekarun baya, ko da ya ke dai bata samu kujeru da yawa ba a majalisar dokoki.

Dan majalisar ya ce dama ya shiga jam'iyyar UKIP ne domin yana son Birtaniya ta fice daga kungiyar Tarayyar Turai, kuma kasancewar yanzu kasar ta dauki hanyar ficewar, burinsa ya cika, bai da wani daili na ci gaba da zama a jam'iyyar.

To sai dai tsohon shugaban jam'iyyar ta UKIP, Nigel Farage, ya bayyana Doughlas Carswell a matsayin mutum mai karambani wanda kuma ya yi zagon kasa wa jam'iyyar, yayin da shi ma shugaban jam'iyyar na yanzu, Paul Nuttall, ya ce dama ba su gamsu da zamansa a jam'iyyar ba.

Tuni wasu 'yan jam'iyyar UKIP suka fara kiraye-kirayen Doughlas Carswell, ya sauka daga kujerar ta majalisa kana a gudanar da sabon zabe na cike gurbi mazabarsa ta Clacton, amma ya ce ba zai yarda da hakan ba.