An sare kawunan 'yan-sanda 40

Image caption JamhuriyarDimokuradiyyar Congo na yawan fama da tarzoma

Rahotanni daga Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo na cewa mayakan sa-kai sun fille kawunan jami'an 'yan-sanda arba'in a wani kwanton-bauna a lardin Kasai dake tsakiyar kasar. Wannan shi ne na baya-bayan nan a jerin kashe-kashen jama'a a lardin.

Masu dauko rahotanni na cewa ana danganta kisan da wata gwagwramayar neman iko da kuma rikcin siyasar kasar ta Congo baki daya, inda shugaba Joseph Kabila ya ci gaba da zama a kujerar mulki duk da cewa wa'adin mulkinsa ya kare.

Harin dai shi ne mafi haddasa hasarar rayuka tun da aka fara samun ayyukan masu tayar da kayar baya a watan Agustan bara.

A cikin wannan mako, Majalisar Dinkin Duniya ta ce jami'an tsaro sun kashe mayakan sa-kai kimanin dari daya, ta kuma bayyana gano manyan kabarbura a yankin na Kasai.

Majalisar ta ce baki daya tashin hankalin na yankin Kasai ya haddasa mutuwar mutane akalla 400 yayin da wasu dimbin mutanen kuma suka bata bat, har yanzu ba a san inda suke ba.