Niger: An sako wadanda aka zarga da juyin mulki

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jamhuriyyar Nijar na daya daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya kuma a cikin sahara ta ke.

Wata kotu a Niamey babban birnin jamhuriyar Nijar ta saki mutane 15 fararen hula wadanda aka zarga da yunkurin kifar da gwamnatin Muhammadou Issouffou.

Mutanen wadanda aka tsare su a gidajen yari daban-daban sama da shekara guda da ta gabata, an yi masu sakin talala ne.

Suna dai musanta zargin da gwamnatin kasar ke yi masu na yunkurin juyin mulki a watan Disamban 2015, wanda bai yi nasara ba.

To sai dai har yanzu ana ci gaba da tsare wasu hafsoshin sojin kasar da ake zargi da hannu a yunkurin na kifar da gwamnatin.

A watan Disaman 2015 ne dai yayin da ake shirye-shiryen gudanar da manyan zabukan jamhuriyar Nijar, shugaban kasar ya fito ya yi shelar cewa an yi yunkurin kifar da gwamnatinsa, daga bisani kuma aka kama mutane da dama galibi 'yan adawa da kuma jami'an tsaro.

Saurari rahoton Tchima Illa Issoufou.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Shugaba Muhammadou Issouffou ne ya yi zargin cewa an yi yunkurin kifar da gwamnatinsa