Turai: An yi zanga-zangar adawa da ficewar Birtaniya

Image caption Ana ci gaba da takaddama kan ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai duk da cewa tuni aka kada kuri'ar raba-gardama

Dubban mutane sun yi zanga-zanga a titunan birnin London domin nuna rashin amincewarsu da ficewar Birtaniya daga kungiyar ta Tarayyar Turai.

An yi macin ne yayin da kungiyar ta EU ke bikin cika shekaru sittin da kafuwa, kana kwanaki hudu kacal kafin lokacin da aka shirya Firayim-Minista Theresa May, za ta bayar da sanarwar dora Birtaniyar a kan hanyar ficewa daga Tarayyar Turai a hukumance ta hanyar amfani da sharadar doka ta 50 wadda ta bukaci hakan.

Daga nan ne za a kwashe kimanin shekaru biyu ana tattaunawa tsakanin Birtaniya da kungiyar EU kan yadda hulda zata kasance tsakanin bangarorin biyu idan Birtaniyar ta kammala ficewa.

Wasu masu zanga-zangar sun shaida wa BBC cewa suna ganin babu alheri a ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Tura, hasali ma sai dai a samu koma baya da kara rarraban kan jama'a, inda daya daga cikinsu ya ce ''Ai doka bata ce dole a yi aiki da sakamakon kuri'ar raba-gardama da aka kada ba, wannan shawara ce kawai ga majalisar dokoki. Don haka bai kamata wannan mataki ya rabani da matsayina na dan-turai ba, matsayin da aka haife ni da shi.''.

Image caption Masu zanga-zanga na cewa rayuwar jama'ar Birtaniya na cikin rashin tabbas game da ficewar kasar daga EU

Masu zanga-zangar goyon bayan hada kan Turai din dun kammala ne a dandalin Majalisar Dokoki, wato wurin da aka kai harin ta'addanci a makon jiya inda mutane hudu suka mutu.

A halin da ake ciki kuma, shuwagabannin kungiyar Tarayyar Turai sun jaddada bukatar hadin kai, yayin wani biki a babban birnin kasar Italiya domin cika shekaru sittin da kulla yarjejeniyar Rome, wadda a karkashinta aka kafa kungiyar tarayyar Turai din.

Kasashe ashirin da bakwai mambobi a kungiyar, sun sa hannu kan wata sabuwar yarjejeniya domin kara martaba yarjejeniyar da ak akulla a alib da dari tara da hamsin da bakwai.

Birtaniya wadda ke shirin fita daga kungiyar ta Tarayyar Turai ba ta hakarci a bikin ba.

A shekarar da ta gabata ne dai jama'ar Birtaniya suka kada kuri'ar raba-gardama inda masu son ficewar kasar daga kungiyar Tarayyat Tura suka samu galaba.