'Dambarwa kan Magu za ta sa wa mutane shakku'

Ibrahim Magu Hakkin mallakar hoto EFCC
Image caption Karo na biyu kenan majalisar dattijan Nijeriya ke ƙin tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin cikakken shugaban EFCC

Wasu masharhanta a Nijeriya sun ce dambarwar da ake yi a kan shugaban riƙo na hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar, Ibrahim Magu ka iya sa wa al'umma shakku a zukata.

Matakin dai ya biyo bayan wata wasiƙa da hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya DSS ta aika wa majalisar dattijan ƙasar ne, wadda ta ƙi tabbatar da Ibrahim Magu a kan shugabancin hukumar.

Wani masanin kimiyyar siyasa a jami'ar Abuja, Dr. Abubakar Kari ya ce abin da ya fito fili shi ne DSS da ma wasu gaggan jami'an gwamnatin (Buhari) na fitar da rahotannin bankaɗa don kada Ibrahim Magu ya kai labari.

Ya ce "yawancin sabbin zarge-zargen (da aka yi wa Ibrahim Magu)kimanin kashi 70 cikin 100, su ne aka miƙa su a watan Janairu, kuma...har shugaban ƙasa ya kafa kwamiti a ƙarƙashin atoni janar wanda shi kuma ya ce an wanke shi."

A cewar masharhancin maganar alaƙarsa (Magu) da wani tsohon babban hafsan sojan ruwan ƙasar da maganar gidan da yake ciki... Abubuwa ne da ya ce a iya saninsa an wanke su.

Ya ce al'amarin tamkar wani zagon ƙasa ne hukumar ke yi ga ƙoƙarin shugaban ƙasa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.

'Yan Nijeriya da dama na kallon Magu a matsayin wani jajirtaccen jagoran yaƙi da cin hanci da rashawa, wanda a ƙarƙashinsa, hukumar EFCC ta gurfanar da wasu jiga-jigan gwamnatin baya.

Dr. Kari ya ce akwai ɗaure kai kan yadda hukumar DSS ta gaza bayar da rahotonta a kan Magu ga shugaban ƙasa, har sai da ta bari ya sake miƙa wa majalisa sunansa don tantancewa.

Ko da yake, wasu ke zarginsa da cewa hukumarsa 'yan adawa kaɗai take takurawa, don kuwa akwai na-kusa da gwamnatin yanzu da ake zargi da aikata cin hanci amma EFCC ba ta iya gurfanar da su gaban shari'ah ba.

Labarai masu alaka