Mun sha wahala da wayar tarho zuwa Nigeria — Bargers

Tsohon shugaban sashen Hausa na BBC Bary Bargers ( Dama )
Image caption Mista Bary Bargers ya ce a tsakanin 1975 zuwa 76 lokacin da suke aiki a BBC, sun sha wahala matuƙa wajen samun layin wayar tarho zuwa Nijeriya.

Wani tsohon shugaban Sashen Hausa na BBC Bary Bargers, ya ce ba za ta yiwu BBC ta ci gaba da watsa shirye-shirye ga nahiyar Afirka ba, ba tare da ta Sashen Hausa ba.

Ya ce ko da yake, tafiya ta yi nisa ga Sashen Hausa amma ba a kai ga ƙarshe ba, don haka ya yi fatan ƙara samun bunƙasa da ci gaba.

Bary Bargers ya ce ya fara karatun digiri a fannin Hausa ne a wata jami'a da ke London, amma aikin da ya yi a Sashen Hausa na BBC ne ya ba shi damar gogewa a Hausa.

Ya ce lokacin da ya yi aiki a Sashen Hausa, aikin bai wuce fassara ba daga Ingilishi zuwa Hausa, sai kuma karanta labarai ko rahotanni.

Mista Bargers ya ce a tsakanin 1975 zuwa 76 lokacin da suke aiki, sun sha wahala matuƙa wajen samun layin wayar tarho zuwa Nijeriya.

Ya ce wakilansu da ke Nijeriya kamar Abba Abdullahi ba sa iya karanta rahotanni a wancan lokaci, sai dai su aika da rubutacce, wani kuma ya karanta a London.

Bary Bargers ya ce abin mamaki ne ganin yadda layin wayar tarho ya fara inganta a jamhuriyar Nijar kafin Nijeriya.

Ya ce ba shakka an samu ci gaba ta fuskar harkokin kayan aiki a yanzu.

Tsohon shugaban Sashen Hausan ta ce ba kamar yanzu ba, da ake samun ra'ayoyin masu sauraro a karanta nan take, su a lokacin sai an shafe tsawon kwanaki kafin su iya samun wasiƙar da mai sauraro ya aiko.

Bargers wanda ya yi aiki a BBC tsakanin 1974 - 1999, ya ce suna amfani da hanyoyin sadarwa kamar Telex ne wajen isar da saƙo a cikin gaggawa, saboda rashin layukan sadarwar wayar tarho.

Labarai masu alaka