Ile-Ife: Babu ƙabilanci a kamen da muka yi — Sufeto Janar na 'yan sanda

IG Hakkin mallakar hoto Idris Kpotun Facebook
Image caption Sifeton 'yan sanda Idris Ibrahim Kpotun ya ce za su hukunta masu laifi

Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya ya yi raddi ga masu cewa an kama Yarbawa ne kadai bayan rikicin da aka yi a garin Ile-Ife na jihar Osun.

Ibrahim Idris ya shaida wa manema labarai cewa duk masu son sanya kabilanci a batun kamen da aka yi suna so ne kawai su karkatar da hankalin 'yan kasar daga laifin da aka aikata.

A cewarsa, "Shi laifi ba shi da fuska ko addini; duk wanda ya yi laifi ko Musulmi ne ko Bayerabe ne ko Bahaushe ne za mu kama shi."

Ya yi wannan bayani ne a yayin da wasu 'yan kabilar Yarbawa ke yin kira da a saki 'yan uwansu da aka kama, suna masu yin barazanar cewa kin yin hakan zai haifar da mummunan sakamako.

A makon jiya ne dai aka kama mutum 35 da ake zargi da hannu a tashin hankalin Ile-Ife, amma daga bisani an saki 15 saboda an gano ba su da laifi.

Da ma dai Sufeto Janar na 'yan sandan ya aike da wata tawaga Ile-Ife domin yin bincike kan rikicin na kabilanci da ya barke a garin.

Rikicin ya barke a tsakanin Hausawa da Yarbawa - a sakamakon gardamar da ta taso tsakanin wata mace Bayerabiya da kuma wani Bahaushe.

Rahotanni dai na cewa an samu salwantar rayuka kusan 40 da dukiya mai yawa.

Labarai masu alaka