Fatana BBC Hausa ta wanzu har Mahadi -Barry Burgess

Image caption Mista Barry Burgess (a bangaren hagu), shugaban BBC Hausa na yanzu Jimeh Saleh (a tsakiya) da kuma Furofesa Phil Jagger, kwararre kan nazarin harshen Hausa ( a bangaren dama)

Wani tsohon shugaban sashen Hausa na BBC,Mista Barry Burgess, ya ce yana fata Sashen Hausa na BBC din zai dawwama kuma ya ci gaba da bunkasa da gabatar da shirye-shirye masu kayatarwa musamman ganin a cewarsa, yadda harshen Hausa ke ci gaba da yaduwa da kuma kokarin kasancewa daya daga cikin 'manyan harsuna a duniya'.

Tsohon shugaban wanda ya yi aiki a BBC Hausa na tsawon shekaru 25, ya ce ya yi imanin ba za ta yiwu ba, BBC dungurugum dinta ta ci gaba da watsa shirye-shirye ga nahiyar Afirka, ba tare da ta Sashen Hausa ba.

Ya ce ko da ya ke, tafiya ta yi nisa ga Sashen Hausa wanda ya cika shekaru 60 da kafuwa a wannan wata, to amma ba a kai ga ƙarshe ba, don haka ya yi fatan ƙara samun bunƙasa da ci gaba.

Barry Burgess wanda a halin yanzu manazarcin harsuna ne, ya ce ya fara karatun digiri a fannin Hausa ne a wata jami'a da ke London, amma aikin da ya yi a Sashen Hausa na BBC ne ya ba shi damar gogewa a harshen Hausa.

Saurari cikakkiyar hirarsa ta Is'haq Khalid a filin Taba Kidi Taba Karatu:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Mista Barry ya yi aiki a BBC Hausa daga 1974 zuwa 1999

Ya ce lokacin da ya yi aiki a Sashen Hausa, aikin bai wuce fassara ba daga Ingilishi zuwa Hausa, sai kuma karanta labarai ko rahotanni.

Mista Burgess ya ce a tsakanin 1975 zuwa 1976 lokacin da suke aiki, sun sha wahala matuƙa wajen samun layin wayar tarho zuwa Nijeriya.

Ya ce wakilansu da ke Nijeriya kamar Abba Abdullahi ba sa iya yin rahotanni ta hanyar nadar muryarsu a wancan lokaci saboda da rashin hanyoyin sadarwa tsakanin London da Nijeriya, sai dai su aika da rubutaccen rahoto, wani kuma ya karanta a London kana a watsa wa duniya.

Mista Barry Burgess ya ce abin mamaki ne ganin yadda layin wayar tarho ya fara inganta a jamhuriyar Nijar kafin a Nijeriya.

Ya ce ba shakka an samu ci gaba ta fuskar harkokin kayan aiki a yanzu.

Tsohon shugaban Sashen Hausan ya ce ba kamar yanzu ba, da ake samun ra'ayoyin masu sauraro a karanta nan take, su a lokacin sai an shafe tsawon kwanaki kafin su iya samun wasiƙar da mai sauraro ya aiko.

Burgess wanda ya yi aiki a BBC tsakanin 1974 - 1999, ya ce suna amfani da hanyoyin sadarwa kamar Telex ne wajen isar da saƙo a cikin gaggawa, saboda rashin layukan sadarwar wayar tarho.