Kotun Masar ta daure mutane 56 saboda kashe 'yan ci-rani 200

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan ci-rani da 'yan gudun hijira na yawan mutuwa a kan hanyar zuwa Turai

Wata kotu a kasar Masar ta yanke hukuncin dauri a gidan yari ga mutane 56 bayan da aka same su da hannu a kifewar wani kwale-kwale mai dauke da 'yan ci-rani. 'Yan ci-rani fiye da 200 ne suka mutu a lamarin wanda ya faru a watan Satumban bara.

An tuhumi mutanen ne da laifukan da suka hada da haddasa hadarin da ya kashe mutune, da rashin wadatattun kayan aikin agaji, da boye mutanen da ake zargi da kuma amfani da jirgin ruwa marar lasisi.

Kwale-kwalen dai ya nitse ne a tekun Bahar Rum, kusa da gabar ruwan Masar watan Satumban shekarar da ta gabata.

Dama 'yan ci-ranin sun nufi kasar Italiya ne a daya daga cikin hanyoyi mafiya hadari da 'yan ci-rani ke bi. An dai ci nasarar ceto 160 daga cikinsu.

Wadanda suka tsira daga hadarin sun ce akwai matukar cunkoso a jirgin ruwan.