Amurka na sasanta manoma da makiyaya a Nigeria

Image caption Makiyaya kan koka da rashin isassun wuraren kiwo, manoma kuma na kukan cewa dabbobi na masu barna

Kasar Amurka ta bayyana aniyarta ta taimakawa wajen shawo kan yawan rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya a Najeriya da sauran kasashen Afirka inda ake samun hasarar rayuka.

Dangane da haka ne ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya yunkura domin sasanta tsakanin manoma da makiyaya a yankin Kudu Maso Yammacin kasar.

Jami'an jakadancin Amurka a Najeriya suna tuntubar bangarorin biyu tare da kokarin gudanar da jerin takuran sulhu a birnin Legas inda wakilan bangarorin dake samun matsalar ta rikice-rikice a yankin Kudu maso Yamma suka halarta.

Image caption Jami'an Amurka na kokarin sulhu a Najeriya

Wakilin ofishin jakadancin Amurkar a game da sha'anin tattalin arziki da siyasa, Mista Thomas Hines, ya ce kasar Amurka ta dukufa wajen ganin an samu zaman lafiya a kasashen Afirka musamman Najeriya.

Ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki da su dauki nagartattun matakan magance matsalar talauci da jahilci da cin hanci da rashawa da kuma bazanar fari, da karancin wuraren kiwo domin kawo karshen yawan rigingimu tsakanin manoma da makiya.

Shi kuma a nasa bangaren, Sarkin Fulani a yankin Kudu Maso Yammacin Najeriya, Alhaji Abubakar Muhammadu Bambado, wanda ya wakilci makiyaya, ya yaba da shirin sulhun na Amurka, amma ya ce matsalar ba a Kudu maso Yamma kadai take ba, ta shafi dukkan sassa na Najeriya ne, don haka ya bukaci Amurka ta fadada shirin.

Image caption Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya na cewa zai ci gaba da shiga tsakani ta hanyar tuntuba da kuma taruka

To sai dai jami'in diflomasiyyar Amurka a Najeriya, Mista Thomas Hines ya ce za su ci gaba da irin wannan yunkuri na sasanta tsakanin al'umomi, musamman manoma da makiyaya, a kudancin Najeriya da ma kasar baki daya.

Daya daga cikin wadanda suka yi jawabi, Imam Shafi'u Abdulkareem, wanda ke daga bangaren al'uma manoma dake yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, ya ce wajibi ne manoma da makiyaya da kuma kabilun daban-daban su hada kansu wuri guda domin ci gaban kasa.

Ya kara da cewa wani abin la'akari shi ne yadda aka samu auratayya tsakanin al'umomin, don haka babu wani dalilin samun tashin hankali a tsakaninsu.

Wakilin BBC Umar Shehu Elleman ya ce rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya kan yi sanadiyar hasarar rayukan mutane da dukiya a jihohi da dama na Najeriya amma dukkan kokarin da aka yi a baya domin magance matsalar ya ci tura inda wasu ke cewa abin na da daure kai.