Ɗamammen wando ya sa an hana mata shiga jirgi

United Airlines Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kamfanin sufurin jirgin sama na United Airlines ya ce tikitin da 'yan matan ke tafiya da shi ne ya buƙaci sai sun yi shigar kamala

Kamfanin jirgin sama na United Airlines na fuskantar gagarumar suka a shafukan sada zumunta, bayan rahotanni sun ce ya hana 'yan mata biyu shiga jirgin saboda ɗAmammen wandon da suka sanya.

Wata 'yar fafutuka Shannon Watts ta ce lamarin ya faru ne ranar Lahadi a wani jirgi da zai tashi daga Denver zuwa Minneapolis.

Ta buga a shafinta na Twitter cewa wani mai tsaron ƙofa a kamfanin ya riƙa "tilasta" wa 'yan matan, ɗaya a cikinsu 'yar shekara 10, su sauya tufafinsu ko kuma su sanya wani mayafi a kan matsattsen wandon.

Shi dai kamfanin ya ce 'yan matan na tafiya ne da wani tikiti da ke buƙatar fasinja ya yi shiga ta kamala.

Shi ma a saƙon Twitter da ya buga, ya ce tikitan 'yan mata sun nuna cewa su ma'aikatan kamfani ne ko kuma matafiyan da ke buƙatar rakiya.

Shannon Watts ta ce 'yan matan su biyar suke tafiya a lokacin, amma aka bar ukun suka shiga jirgi bayan sun ɗora wani tufafin a kan ɗamammen wandonsu.

Labarai masu alaka