Ba mu yarda da ilmin jima'i ba - Malaman Nijar

Image caption Akasarin jami'in ilmi da BBC ta yi ƙoƙarin jin ta-bakinsu a kan zarge-zargen malaman sun ƙi cewa uffan

Malaman addinin musulunci a jamhuriyar Nijar sun bayyana damuwa game da koyar da ilmin jima'i a makarantun Boko da kuma hana auren wuri.

Malaman sun bayyana haka ne, yayin wani taron da suka gudanar kan halin taɓarɓarewa da ilmin ƙasar yake ciki a babban masallacin Juma'a na birnin Niamey.

Ɗaya daga cikin malaman da suka shirya taron, Malam Muhammad ya ce "kowacce jiha tana ɗaukar malamai ana horas da su a kan tafiyar da wannan tsari na koyar da batsa."

"Wannan abu ya ba mu mamaki, ya tayar da mana da hankali."

Babban malamin ya ce abin dubawa ne bisa la'akari da ganin yadda ake yunƙurin sake dawo da kundin hana auren wuri.

Ya ce malaman suna jin ƙishin-ƙishin game da ƙoƙarin sake mayar da kundin zuwa majalisa.

Malam Muhammad ya ce wajibi ne 'yan majalisa da hukumomin ƙasar su tashi tsaye don kare mutunci da addini da kuma tarbiyyar al'umma.

Taron ya kuma yi kira ga malaman makarantun Boko da gwamnati su yi ƙoƙarin sasantawa da juna don kyautata makomar ɗaliban ƙasar.

Sun kuma yi addu'ar Allah ya jiƙan dakarun sojan Nijar da suka riga mu gidan gaskiya a bakin aikin kare al'umma da mutuncin ƙasar.

Labarai masu alaka