Kun san kalmomin farko a Sashen Hausa na BBC?

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Saurari kalmomin da aka fara amfani da su a BBC Hausa

Wani tsohon ma'aikacin Sashen Hausa na BBC, Zakari Mohammed ya ce shirye-shiryen Sashen na farko sun fi mayar da hankali kan abubuwan ban sha'awa na mutanen Ingila da sauran rayuwar Turawa.

Malam Zakari Mohammed ya ce ya fara aiki da Sashen Hausa na BBC ne bayan ya halarci bikin samun 'yancin kan ƙasar Ghana, lokacin da yake karatu a London, inda ya buƙaci a ba shi dama ya gabatar.

Ya ce a matsayinsu na ɗalibai sukan yi nazarin wasu abubuwan burgewa game da rayuwar Turawan Ingila, kuma su rubuta kafin a ba su damar gabatarwa.

Ma'aikacin BBC na farko-farkon ya ce kamar sauran takwarorinsa da suka fara gabatar da shirye-shirye farkon buɗe Sashen Hausa ya je Ingila ne don karanta fannin shari'ah, abin da ya ba shi damar yin aiki da Sashen Hausa na BBC.

Zakari Mohammed ya ce sai daga baya ne aka ɗauki rukunin ma'aikatan BBC na farko da suka hadar da Marigayi Balarabe Fatika da Umaru Dikko da Alhaji Adamu Muhammad.

Ya ce "idan dai ba ni ne na farko da na fara yi wa BBC aiki da Hausa ba, ba shakka ina cikin mutum goma na farko."

A ranar 30 ga watan Maris ɗin 1957 ne, Sashen Hausa na BBC ya fara gabatar da shirye-shiryensa ga ƙasashen duniya.

Shirin Sashen Hausa na BBC da aka fara gabatarwa ya fara ne da "London take kira. A yau BBC ta London, ta samu damar yi ma mutanen Afirka ta yamma waɗanda suke sauraronta magana a cikin ɗaya daga cikin harsunansu..."

Labarai masu alaka