'Babu maganin cutar Endometriosis da ta gallabi mata'

mata da dama na fama da cutar Endometriosis Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ba safai likitoci ke iya gano cutar da wuri ba

Cutar Endometriosis na aukuwa ne a lokacin da wasu kwayoyin halitta masu kama da na cikin mahaifa ke tsirowa a wani bangare na jikin mace.

A ko wane wata kuma, wadannan kwayoyin halitta na kwaikwayon abubuwan da kwayoyin halittar da ke taimaka wa mata wajen zubar da jini haila, ta yadda su ma suke fashewa su saka mace ta rika zubar da jini.

Yayin da jinin haila ke iya fita daga jikin mace, shi wannan jinin ba shi da mafita.

Ba safai likitoci ke iya ganowa da wuri cewa mace na fama da irin wannan lalular ba, kuma ba a yadda a bai wa mata masu fama da irin wannan cutar kulawa ba, a cewar masu aikin kiwon lafiya.

Ko wacce mace daya cikin goma na fama da wannan ciwon, kuma ya kan haifar da tsananin ciwo, da jin zafi wajen jima'i da kuma shiga yanayin damuwa.

Sama da mata 2,600 sun yi magana da kungiyar All Parliamentary da ke kula da lafiyar mata, inda kashi 40 cikin 100 ke cewa sai da suka ga likita sau goma sannan daga bisani aka gano cewa cutar Endometriosis ke damunsu.

Wasu da dama sun ce da kansu suka yi bincike suka gane cutar.

Menene maganin wannan cuta?

A halin yanzu babu maganin wannan cuta amma kuma ana iya magance alamominta.

An sanya wa Amy wani abu mai kama da zobe kuma wannan abin ya taimaka mata.

An yi wa wasu tiyata domin a cire musu amma kuma akwai yiwuwar zai sake tsirowa.

Amma wasu da yawa magungunan rage radadi suke sha kawai.

A baya an shaida wa wasu matan cewa cire mahaifarsu baki daya ko kuma haihuwa zai iya magance cutar, amma babu wata shaida da ke nuna hakan.

Sabon rahoton ya ce a yanzu haka ba a yarda a bai wa mata masu fama da irin wannan cutar wata kulawa ba, inda kwararru a bangaren lafiya ke kin kula su.

Me yasa ake dadewa kafin a gano cutar?

Image caption Kafin a gano cutar sai an duba halittun da ke cikin mutum

Ya kan dauki tsawon shekara bakwai zuwa bakwai da rabi kafin a gano cewa mace na dauke da wannan cutar.

Kafin a gano cutar, sai an yi wa mace abin da ake kira Laparoscopy, inda ake duba halittun da ke cikin mutum. Ana sanyawa mace kamara a cikin kugunta domin a duba alamun cutar endometriosis.

Farfesa Helen Stokes - Lampard na kwalejin Royal ta likitoci ta ce cuta ce mai sarkakaya da ba safai likitoci ke saurin gano ta ba.

Farfesa Helen ta shaidawa shirin BBC na NewsBeat cewa Likitoci na fuskantar kalubale biyu, na iya gano cutar da ke da alamu daban-daban.

"Kuma da a ce zamu danganta kowa da alamun cutar da ka iya yiwuwa endometriosis ce, da asibitoci sun cika kuma da hakan ba zai taimakawa marasa lafiya dama a asibitocin ba.

Da zai kasance ana yi wa wasu marasa lafiya tiyatar da basu bukata."

A yanzu masu fafutuka suna kira da a wayar da kan mata a makarantu a kan kula da lafiyarsu a lokutan da suke haila da kuma kara bai wa likitoci horo mai inganci.

Ya ce kashi 42 cikin 100 na matan da aka yi hira da su sun yi ikrarin cewa, likitoci ba su daraja kima da mutuncinsu.

Labarai masu alaka