An ɗibga gagarumar satar sisin gwal a Jamus

Canadian Coin Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Irin wannan danƙareren sisin gwal ne mai kan Sarauniya ne ɓarayi suka arce da shi daga gidan kayan tarihi

An sace wani danƙareren sisin gwal mai ɗauke da hoton sarauniya da ya kai darajar $4m kimanin Naira 1.5bn a wani gidan adana kayan tarihi na ƙasar Jamus.

Sisin gwal ɗin asalinsa daga ƙasar Kanada darajarsa ta ainihi dala miliyan ɗaya ce, amma saboda nauyinsa ya kai kilogram 100 na zinariya zuryan karat 24 a yanzu farashinsa ya fi gaban haka nesa ba kusa ba.

Da tsakar dare ne aka dirga gidan adana kayan tarihin Bode a birnin Berlin aka sace shi.

Ba a iya tantance yadda ɓarayin suka yi wa na'urorin tsaro layar zana suka je suka ɗauke danƙareren sisin ba, wanda faɗinsa ya kai rabin mita.

An yi imani cewa an tafka wannan sata ce ranar Litinin da misalin ƙarfe 03:30 cikin tsakar dare.

Sisin gwal ɗin yana da matuƙar nauyin da ya fi ƙarfin mutum ɗaya, 'yan sanda sun yi imani cewa ɓarayin sun shiga gidan ne ta wata taga.

Daga bisani, an gano wani tsani da ake kyautata tsammanin ɓarayin sun yi amfani da shi wajen aikatar satar a kusa da ginin.

Wani mai magana da yawun 'yan sanda, Winfrid Wenzel ya ce daga bayanan da suke da su ya zuwa yanzu sun yi imani cewa ɓarawon ko mai yiwuwa ɓarayin, sun karya wata taga a bayan gidan kayan tarihi kusa da layin jirgin ƙasa.

Labarai masu alaka